Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Datti Baba-Ahmed, ya ce dole a tambayi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, game da iƙirarin da ya yi cewa Gwamnatin Tarayya na biyan ‘yan bindiga kuɗi.
Yayin hira da gidan talabijin na Channelsa ranar Talata, Baba-Ahmed ya ce wannan magana babba ce, bai kamata a yi watsi da ita ba.
- Sabuwar Ajandar Mulkin Duniya Ta Nuna Alhakin Da Kasar Sin Ta Dauka
- Shugaban Uganda: Jarin Sin Na Taimakawa Wajen Bunkasa Ci Gaban Kasashen Afirka
Ya kuma soki ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA) saboda ƙin amincewa da zargin.
A baya, El-Rufai ya yi iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya da ta Kaduna suna bai wa ‘yan bindiga kuɗaɗen wata-wata tare da kayan abinci.
Duk da cewa NSA da gwamnatin Kaduna sun musanta zargin, Baba-Ahmed ya bayyana cewa El-Rufai ya kamata ya yi bayani a gaban jami’an tsaro da kuma kotu.
Domin ya ce wannnan matsala ce da ta shafi ƙasa, kuma ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanin halin da ƙasar ke ciki.
A cewarsa wannan babban zargi ne, don haka bai kamata a manta da shi ta hanyar yin jawabi ba tare da wasu gamsassun hujjoji ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp