Shugaban Kungiyar Maj’ma’ul-Ahababul-Sheik Ibrahim Inyass (r), Sheikh Sharif Muhammad Dallami Zariya ya bukaci gwamnati ta kula da marayun da aka bari a mummunan hadarin mota da ya faru a karamar hukumar Lere ta Jihar Kaduna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an sami faruwar wani mummunar hadarin mota a garin Lere lokacin da wata tirela ta danne mota kirar J5 da take dauke da mu-tane kimanin 73. Lamarin ya rutsa ne da mutanen garin Kwandari yayin da suka fito zuwa garin Saminaka taron Maulidin Fiyayyen Halitta Annabi (SAW), wanda aka fara tun daga farkon watan Rabi’ul Auwal na wannan shekar 2024.
- An Kashe Jagororin ‘Yan Bindiga, Sani Black Da Kachalla Makore A Zamfara
- Katsina Za Ta Gudanar Da Jarabawar Tantancewa Ga Shugabanni Da Malaman Sakandire
Tawagar kungiyar Maj’ma’ul-Ahababul-Sheik Ibrahim Inyass (r) karkashin jago-rancin Sheikh Sharif Muhammad Dallami Zariya ta kai ta’aziyya a wannan gari domin jajanta wa al’ummar yankin kan wannan mummunar ibtila’i.
Sheikh Sharif wanda shi ne limamin masallacin Juma’a na Realway Sabon Gari Zariya da ke a Jihar Kaduna, ya ce daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu sun bar ‘ya’ya wanda ya kamata gwamnati ta kula da su, domin ceton marayu a cikin al’umma.
Sakataren karamar hukumar Lere, Honorabul Saifullahi Usman, ya tabbatar da faruwar hadarin a yayin da yake karin haske ga manema labarai a gidan sarkin ga-rin na Kwandari, yayin da jama’ar garin suka tarbi tawagar kungiyar Maj’ma’ul- Ahbabul-Sheik Ibrahim Inyass na kasa da ya ziyarcesu don jajantawa.
Ya tabbatar da rasuwar mutane 33, sannan mutum 27 suna kwance a asibiti rai ga hannun Allah. Ya kuma nuna alhininsa tare da kira ga gwamnati karamar hukuma da na jiha har zuwa tarayya baki daya da su duba lamarin kuma su dauki matakin tausaya wa marayun da iyayensu suka rasa rayukansu a wannan hadari.