Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai don gudanar da aikin gina kasar nan.
A cikin sakonsa na barka da sallah da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura wajen Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasar nan su dukufa wajen samar da hadin kai a tsakaninsu.
- Sallah Karama: Kada Mu Cire Kauna Ga Nijeriya, Mu Dage Da Addu’o’i — Garo
- Wang Yi Ya Yi Karin Haske Kan Shawarwarin Sin Na Warware Batutuwan Dake Jan Hankulan Sassan Kasa Da Kasa
Shugaba Tinubu wanda ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya da ma duniya baki daya murna, ya kuma yi addu’ar Allah Ya karbi ibadun da aka gabatar.
A cewarsa hanya daya da kasar nan za ta dawo kan turba shi ne cusa kishin kasar a zukatan al’umma.
Ya ce hakan zai samu ne idan al’ummar kasar nan suka hade kansu waje daya tare da watsar da bambance.