Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya bukaci jami’an tsaro da su sake saka ido sosai wajen ganin cewa an yi zabe lafiya.
Abba, ya bayyana haka ne a mazabarsa da ke uguwar Chiranci a karamar hukumar Gwale, bayan ya kada kuri’arsa.
- ‘Yansanda Sun Ceto Ma’aikatan INEC 19 Da Aka Sace A Imo
- Yadda Wakilan Jam’iyya Ke Siye Mutane Da Atamfa A Kano
Ya ce, ya zama dole jami’an tsaro su sake dagewa wajen ganin ba a samu hargitsi ba a lokacin zabe ba.
Sannan ya jinjina wa jami’an tsaron bisa rawar da suke takawa wajen ganin an yi zaben lafiya an gama lafiya.
Abba, wanda ya yi takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya ce jam’iyyarsa ta NNPP ce za ta samu nasara a wannan zaben.