• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya

by Leadership Hausa
3 weeks ago
Malamai

A yayin da duniya ke fama da karancin Malaman Makarantar Boko, a nan za a iya cewa, wannan lamarin ya fi yin kamari a kasar nan, wanda hakan ya zama wata barazana ga yunkurin da ake yi domin a cimma burin muradun karni, wato SDG 4 musamman domin a samar da ingantaccen ilimin zamani, nan da 2030. Hukumar UNESCO ma, ta ankarar da wannan barazar da ake fusnkanta a fadin duniya na karancin Malama. Ana dai ganin, nan da 2030, duniya na bukatar karin Malaman Makaranta miliyan 44, tun daga daga matkin Firamare zuwa na Sakandare. Ana bukatar wannan adadin na Malam ne, domin a cimma kurin da ake da shi, na samar da Malaman wanda akalla za su rubanya daga kaso 4.62 da ake da su a 2015 zuwa kaso 9.06 a 2022. Sai dai, a gefe daya, Nijeriya na ci gaba da fuskantar kalubalen yara da suka dai zuwa Makarantun Boko, inda aka kiyasata a 2024, yawansu ya kai kimanin miliyan 18.3. Kazalika, akwai bukatar a kara mayar da hankali wajen daukar Malamai aiki da kuma inganta albashinsu, tare da kuma kirkiro da ingantattun sauye-sauyen da zu kai fannin ilimin kasar, ga tudun muntsira.

Ci gaba da samun karancin Malamai da ake fuskanta a fadin duniya, na haifar da koma baya, ga fannin ilimi. Misali, idan aka yi dubi da wani rahoto na fadin duniy da UNESCO ta fitar a watan Afirilun 2025, ya nuna cewa, a Tarayyar Turai da kuma a Anurka ta Tsakiya, duk da irin intanncen tsarin ilimi da suke da shi, suna fuskantar karancin daukar Malamai. Wannan kalubalen, ya haifar da samun cunkoson dalibai a Aji da kuma rashin sakamakon da ake bukata na samar da ilimin.

  • Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
  • Salon Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin: Hanya Ce Mallakar Kasar Sin Wacce Kuma Ta Sada Duniya

Bugu da kari, hakan ya nuna azahiri, a kasashen da ake shelanta cewa, sun ci gaba, amfi samun wannan gibin, musaman duba da yadda kasashen ke ci gaba da fuskatar matsin tattalin arziki da rashin horas da Malamai da kuma biyan albashin da bai taka Kara ya karya ba sauransu.

Hakazalika, bullar annobar Korona, ta kara dagula al’amura, wanda hakan ya janyo yara dalibai, miliyan 84 suka dakatar da zuwa Makarantusu domin daukar darasi.

A bangaren Nijeriya kuwa, wasu sassan kasar na ci gaba da fuskantar kalubalen barkewar rikice-rikice da talauaci da kuma yin shakulatin bangaro da fannin Ilimin Boko.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma wasu lamuran da suka shafi al’ada a fadin kasar, wanda ya kai kaso 15.

Misali, yankin Arewa Maso Gabas, kacal irin wadannan hare-haren babu kakkautawa da mahara ke kai wa ya dakatar da yara miliyan biyu daga zuwa Makaranta inda hare-haren suka lalata gine-genen Makarantu da dama hakan kuma ya kara haifar da karancin Malaman.

Malamai 915,913 kacal ne a matakin karatun Firamare ke koyar da dalibai miliyan 31.7 wanda hakan ke ci gaba haifarwa da bangaren koyarwa, nakasu.

A nan za a iya cewa, matakan Makarantun Firamare, ba fuskanta karancin Makamai sama da 165,000 wanda musamman lamarin, ya fi yin kamari a yankunan Karkara tare da kuma janyo babban gibi a bangaren samar da ingantaccen ilimi.

Kazalika, a cikin kasafin kudi na shekara-shekara, Gwamnati na kebewa fannin ilimi kaso biyar zuwa kaso tara ne, wanda wannan kaso, ya gaza da shawarar da UNESCO ta bayar na a warewa fannin kaso daga 15 zuwa 20, inda hakan ya haifar da samun gazawar kara daukar Malaman aiki.

Wannan karancin na daukar Malaman, ya nuna karara na irin gadawar Gwamnatin, inda a gefe daya kuma ake biyan Malaman can Albashi kalilan da jinkirin biyansu da rashin samar masu da kyakyawan yanayi na koyarwa, wanda hakan ke tilasata su, yin kaura zuwa wasu kasashen duniya inda za a biya su da gwabi.

A kwanukan baya, an samar da wasu shirye-shiye misali, a jihohi kamar irinsu, Anambra da Enugu, ba daukar Malamai 5,000 aiki tare da kuma ware kaso 33 a cikin kasafin kudi na 2025, amma batun wanzar da lamarin a nan ne, natsalar ta ke.

A gefe daya kuma Arewacin kasar na ci gaba da fuskantsr kalubalen tsarin Almajiri da ke da watan gaririya a kwararo-kwararo, ba bu ilimin Boko.

Da farko a nan, muna bayar da shawara da a kaddamar da daukar Malamai a daukacin fadin kasar, musamman kwararru.

Za a iya ci gaba da fuskantar jahilci a kasar inda hakan kuma zai safi fannin tattalin arziki tare da rashin samun daidaito, matkar, ba a dauki matakan gaggawa na magance wadannan matsalolin ba.

Ya zama wajibi jihohin kasar nan su yi hadaka da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta rungumar tsarin zamani irin na kasar Rwanda na magance matsalar da kasar ta Rwanda ta fukasta na karancin Malamai a baya wanda hakan ya bai wa kasar damar kai wa kso 98.

Irin wannan tsarin zai bai wa Nijeriya damar ciki gibin da ake da shi na dalibai guda 165,000, tare da kuma ingnata alawus-alawsu din Malaman da ke koyarwa a yankunan karkara.

Kazalika, ya kamata a kara inganta jin dadi da walwalar Malaman tare da kuma basu dauki, ga bangaren kula da lafiyarsu.

Hukumar ta UNESCO, ta kuma bayar da shawara da a rinka bai wa Malaman horo da samar masu da kayan aiki, domin a rage yawan yadda suke fita ketare, neman aikin yi.

Hakazalika, Hukumar da ke Kula da Yiwa Malaman Makaranta Rijista ta Kasa wato TRCN, ta mayar da hankali wajen ganin ana daukar kwararrun Malamai aiki.

Akwai bukatar a samar da sauye-sauye tare da kara zuba kudade a fannin ilimi wanda zai kai ga akalla an zuba kaso 15 a cikin kasafin kudi na kasa, kamar yadda Gwamnati ta yi alkawri a 2021, sai dai, duk ba a cika wannan alkawarin ba.

Ya kamata a samar da shirye-shiyen magance matsalar yaran da ba sa zuwa Makaranta kamar yadda Bankin Dniya yak ebe kudi har dala miliyan 700, domin tallafawa karatun ‘ya’ya mata

Bugu da kari, ya kamata a yi koyi da tsarin Malamai irin na kasar Finland ko kuma na kasar Singapore wanda ake daukar Malaman bisa cancanta.

Wannan Jaridar ta mayar da hankali wajen ganin ana gudanar da shugabanci na gari, inda take shawartar Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamnatocin jihohi da kuma ‘Yan Majalisar Kasar da su dauki matakan gaggawa, domin magance barazanar karancin Malamai a kasar.

Matsalar ta karancin Malaman da duniya ke fuskanta, ta zama tamkar wata izina ce, ga kasar nan, domin kasar ta shi tsaye, ta magance wannan barazanar.

Baya ga kula da Malaman ya kuma kamata a mayar da hankali a kan makomar daliban, musamman domin kar batun na cimma muradun karni na SDG 4, ya zama tamkar tatsuniya.

Batun kawo uzuri kan wannan barazanar abu ne wanda za a iya cewa, bai ma wani taso ba, domin dole ne a fara daukar matakai na gaba, idan kuma bah aka ba, yaran masu tasowa, za su kasance, a cikin duhun jahilici.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka
Manyan Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja
Manyan Labarai

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja
Manyan Labarai

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Next Post
Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
katsina

Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu

October 17, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

October 17, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
Abduljabbar

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.