Abokaina, ko kun karanta bayanin da shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta a gefen taron sauyin yanayi na COP27, wanda aka buga shi kan shafin yanar gizo na jaridar Washington Post ta kasar Amurka?
Na karanta bayanin, kuma na ji yadda shugaban ya nuna rashin gamsuwa, da takaici, inda ya soki kasashen yamma bisa rashin sauke nauyinsu.
A cewar shugaban, ko da yake kasashen yamma sun yi alkawarin samar da tallafi na dala biliyan 100 ga kasashe masu tasowa a kowace shekara, don taimaka musu wajen tinkarar batun sauyawar yanayi, amma ba su taba cika alkawarin ba.
Har ila yau, a wajen taron COP27, an nanata bukatar biyan diyya ga kasashe masu tasowa, bisa hasarar da suka samu sakamakon sauyin yanayin duniya, amma duk da haka kasashen yamma sun yi shiru.
Na fahimci maganar shugaba Buhari da fushinsa, saboda nahiyar Afirka tana shan wahalar matsalolin sauyin yanayi sosai, ko da yake iska mai dumama yanayin da nahiyar ke fitarwa ba ta da yawa.
A daura da haka, kasashen yamma su ne suka fi samar da iska mai gurbata muhalli cikin shekaru kimanin 200 da suka gabata, kana zuwa yanzu sun fi samun kudi da fasahohi da za su iya amfanar kasashe masu tasowa. Amma duk da haka ba su son sauke nauyin dake bisa wuyansu.
Sa’an nan rashin sauke nauyin na kasashen yamma, bai tsaya kan tsumulmularsu ba, har ma ya shafi wadannan fannoni:
Da farko, manufar da kasashen yamma suka gabatar ta rage fitar da iskar dumama yanayi, ba ta dace da yanayin da kasashen Afirka suke ciki ba.
Saboda nahiyar Afirka ta riga ta kasance yankin da ke fitar da mafi kankantar iskar Carbon. Abun da kasashen Afirka suke bukata shi ne karfafa kwarewarsu a fannin tinkarar bala’u, da kula da jama’ar da iftila’u suka ritsa da su, maimakon daidiata tsarin makamashi ba tare da lura da matsi a fannin tattalin arziki ba.
Na biyu, shi ne kasashen yamma na neman yin amfani da batun sauyawar yanayi wajen kare moriyarsu, har da a nahiyar Afirka. Misali, manufar karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin da suke cewa wai ba irin na kare muhalli ba ne da kungiyar kasashen Turai ta EU ta fara aiwatarwa a bara, tana haifar da karin kudin shiga har Euro biliyan 5 zuwa 14 ga kungiyar EU a duk shekara, duk da cewa manufar ba ta dace da gatan da wasu kasashen Afirka suka samu, a fannin fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin nahiyar Turai ba.
Hakika, bisa karfin tattalin arzikin kasashen yamma, da ingancin fasahohinsu, za su iya taimakawa kasashen Afirka a fannoni daban daban. Idan har mun dauki hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar tinkarar batun sauyin yanayi a matsayin misali: Kasar Sin tana raba bayanan taurarin dan Adam tare da kasashen dake kudancin nahiyar Afirka, da ba da tallafin nau’rorin binciken yanayi masu sarrafa kansu ga kasashen Comoros, da Kenya, da taimakawa kasashen dake yankin Sahel, irinsu Niger da Burkina faso, wajen dasa itatuwa na kare iska, da dai sauransu. Ban da haka, fasahar noman sabon nau’in shinkafa da kasar Sin ta koyar a kasashen Najeriya, da Madagascar, da dai sauransu, ta sa ana samun damar tabbatar da samun isashen abinci, yayin da ake fama da bala’i.
Haka zalika, kamfanonin kasar Sin sun gina tashoshin samar da wutar lantarki ta yin amfani da zafin rana da karfin iska, a kasashen Kenya da Afirka ta Kudu, wadanda suke ba da taimako ga al’ummun kasashen, a kokarinsu na kyautata zaman rayuwa, da kare muhallin halittu.
Ta hanyar kwatanta hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, za mu iya gane cewa, kasashen yamma ba su nuna sahihanci sosai ba.
Kullum suna neman jagorantar aikin tinkarar sauyawar yanayi na duniya, amma sakamakon da suke samarwa ba shi da yawa, sakamakon yadda suke tsumulmular raba moriya ga kasashe masu tasowa.
A gani na, ya kamata kasashen yamma su kara nuna sahihanci, da daukar karin takamaiman matakai na taimakawa kasashen Afirka, saboda hakan ne kadai zai dace da matsayinsu na kasashe masu sukuni. (Bello Wang)