• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Kasashen Yamma Su Yi Hangen Nesa Game Da Tasirin Rikicin Ukraine Kan Kasashe Masu Tasowa

byCMG Hausa
3 years ago
Kasashen yamma

Tuni farashin kayayyakin amfanin gona ya yi tashin gwauron zabi a sassan duniya daban daban, sakamakon rikicin Rasha da Ukraine, wanda a yanzu ya zarce watanni uku da barkewa.

Alkaluman shirin samar da abinci na MDD sun tabbatar da cewa, duniya ba ta taba ganin kalubalen tsadar cimaka sama da na wannan lokaci ba, tun bayan yakin duniya na biyu, lamarin da kuma ke zuwa a gabar da duniya ke fuskantar tasirin annobar COVID-19, wadda ita ma ta haifar da komadar tattalin arzikin duniya.

  • Jawabin Xi Jinping Ya Kara Azama Kan Aiwatar Da Shawarar Bunkasa Duniya

Yayin da kasashen yammacin duniya ke ta kokarin dora alhakin hauhawar farashin kayayyakin amfanin gona ga kasar Rasha, su ma a nasu bangare sun taka rawar gani wajen ingiza girman wannan matsala.

Ga misali, shi kan shi rikicin Rasha da Ukraine, kasashe biyu masu fitar da tarin albarkatun gona ga sassa daban daban na duniya, ya samo asali ne sakamakon kokarin fadada ikon kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabashin turai. Kuma duk da yunkuri da aka yi na hawa teburin shawara tsakanin Rasha da Ukraine, Amurka a nata bangare, ta yi ta kokarin rura wutar rikicin ta hanyar samarwa Ukraine makamai domin tunkarar Rasha, wanda hakan ke kara tsawaita mummunan tasirin tashin hankalin.

A zahiri, tsawaitar wannan tashin hankali zai ci gaba da ingiza asarar da Rasha da Ukraine za su kirga, a hannu guda kuma, hakan zai haifar da kamfar abinci a sassa masu yawa na duniya, musamman kasashe masu tasowa, dake dogaro sosai kan cimakar da ake fitarwa daga kasashen biyu.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Ko shakka ba bu, yunkurin Amurka na kakaba takunkumin cinikayyar albarkatun gona da takin zamani da kasar Rasha ke fitarwa, ya haifar da hauhawar farashin cimaka da kaso sama da 30 bisa dari a kasashe masu tasowa.

Irin wadannan kasashe masu tasowa, da sauran masu raunin tattalin arziki, na shan matsin lambar rayuwa, sakamakon manufofin takara, da kokarin tabbatar da iko na wasu kasashen yamma, wannan yanayi ne da bai dace ba, domin kuwa, kamata yayi manyan kasashen yamma masu karfin fada a ji, su taimaka wajen fitar da kasashe masu tasowa daga wahalhalu, maimakon aiwatar da matakai na kara jefa su cikin mawuyacin hali. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Yadda Wata Budurwa Ta Yi Garkuwa Da Kanta

Yadda Wata Budurwa Ta Yi Garkuwa Da Kanta

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version