Shugabar Rukunin Kamfanin LEADERSHIP, Hajiya Zainab Nda-Isaiah, ta ce bai kamata a riƙa ɗaukar lambobin yabo a matsayin abun karramawa kawai ba, ya kamata su zama hanyar ƙarfafa gwiwar mutane su yi ƙoƙari wajen kawo sauyi a ƙasa.
Da ta ke jawabi a Taron Shekara na 2025 da Taron Bayar da Lambar Yabo na Kamfanin Jaridar LEADERSHIP a Abuja, ta ce burin taron shi ne ƙarfafa wa ‘yan Nijeriya wajen duba abin da za su iya yi don ci gaban ƙasa, musamman a wannan lokaci da ake cikin tsaka mai wuya.
- Hafsan Soji Ya Gana Da Shugabanni A Filato Kan Hare-haren Da Suka Yi Ajalin Mutane
- An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6
“Ba na ganin cewa lambobin yabo ya kamata su tsaya ne a kan karramawa kawai,” in ji ta.
“Ya kamata su zama hanyar ƙarfafa wasu, musamman a irin wannan lokacin da tattalin arziƙin duniya ke cikin mawuyacin hali.”
Taron na bana ya kasance cikin shagulgulan cikar Jaridar LEADERSHIP shekaru 20 da kafuwa, kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne babban bako mai jawabi a wajen.
Hajiya Zainab ta kuma tuna da marigayi mijinta, Sam Nda-Isaiah, wanda ya kafa LEADERSHIP a shekarar 2004.
“Tun shekaru ashirin da suka gabata, wanda ya kafa wannan jarida ya shigo harkar wallafa da wani babban buri — Don Allah da kuma ƙasar nan.
“Wannan buri har yanzu yana jagorantarmu, kuma da yardar Allah za mu isar da shi zuwa ga ƙarni na gaba,” in ji ta.
Ta ƙare da jan hankalin kowa da ya yi tunani a kan irin gudummawar da zai bayar wajen gina Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp