Makomar mai koyarwa Erik ten Hag a Manchester United ita ce abar da ake tattaunawa musamman ga masu sharhi a kan kwallon kafa da kuma magoya bayan kungiyar ta kasar Ingila.
Sai dai har yanzu akwai wadanda suke ganin akwai bukatar a sake ba wa dan kasar Holland din dama zuwa kakar wasa ta gaba domin a ganinsu zai iya dawo da kungiyar hayyacinta.
- Mukalar Shugaba Xi: Hakika Kasar Sin Ba Ta Yi Wa Duniya Rowar Kaifin Basirarta Ba
- Gwamnan Zamfara Ya Sauke Nauyin Bashin Haƙƙoƙin Ma’aikata Na Fiye Da Naira Biliyan 4
Manchester United ta kasa samun gurbin komawa cikin masu fatan buga gasar Zakarun Turai a badi, bayan da Crystal Palace ta yi raga-raga da ita da ci 4-0 ranar Litinin a filin wasa na Selhurst Park.
Kungiyoyin sun kara a gasar mako na 36 a babbar gasar firimiya ta Ingila da suka fafata a Selhurst Park kuma Crystal Palace ta fara cin kwallo ta hannun Michael Olise daga baya Jean-Philippe Mateta ya kara ta biyu saura minti biyar su je hutun rabin lokaci.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Crystal Palace ta kara zura kwallaye biyu a ragar United ta hannun Tyrick Mitchell da kuma Michael Olise, wanda ya ci ta biyu a karawar. Wannan shi ne wasa na uku da suka fuskanci juna, bayan da Manchester United ta fara cin 3-0 a League Cup cikin Satumba kuma kwana hudu tsakani Palace ta shiga Old Trafford ta doke United 1-0, inda Joachim Andersen ne ya ci kwallon a minti na 25.
Wannan shi ne karo na biyu da Palace ta zura kwallaye da yawa a ragar Manchester United tun bayan 5-0 ranar Asabar 16 ga watan Disambar 1972 tun a gasar rukunin farko. Kawo yanzu a wannan kakar an zura kwallo 81 a ragar Manchester United a dukkan fafatawa a bana, kakar da kwallaye da yawa suka shiga ragarta tun 81 da aka dura mata a 1976 zuwa 1977.
Da wannan sakamakon Manchester United tana ta takwas a teburin Premier League da maki 54, iri daya da na Chelsea ta bakwai, wadda ta ci West Ham 5-0 ranar Lahadi, sai
Crystal Palace ta hada maki uku kenan ya zama 43 tana nan a matakinta na 14 a kasan teburin Premier da tazarar maki daya tsakaninta da Fulham ta 13. Sauran wasa biyu ya rage a gaban Crystal Palace da za ta je Wolberhampton a karshen mako, sannan ta karbi bakuncin Aston Billa a wasan karshe yayin da United kuwa wasa uku ne a gabanta, wadda za ta karbi bakuncin Arsenal da kuma Newcastle, sannan ta karkare da zuwa gidan Brighton.
United tana fatan daukar kofi a bana shi ne FA Cup da za ta fafata da Manchester City a wasan karshe.
Ina Matsalar Take?
Manchester United ta saka dukkan ‘yan wasanta a kasuwa, bayan da take fatan hada kudin da za ta bunkasa kungiyar karkashin INEOS daga badi kuma United ta kashe Yuro biliyan 1 a shekaru da yawa wajen sayen ‘yan wasan dake buga mata wasa, amma ta kasa taka rawar gani a kaka da yawa har da karkashin mai koyarwa Erik ten Hag.
Wannan ce kaka ta biyu da Ten Hag ya ja ragamar United, wanda ya dauki Carabao Cup a bara da samun gurbin Champions League a bara amma sai dai a bana an yi waje da kungiyar daga gasar Zaratun Turai cikin rukuni, sannan aka fitar da ita a Carabao Cup, bayan rashin nasara a hannun Newcastle United.
 Sannan da yake kungiyar ba za ta samu gurbin shiga Champions League a badi ba, ya zama wajibi ta rabu da wasu ‘yan kwallon a bana, domin ta samu gudanar da kungiyar kan cin riba.
Albashin da Manchester United kan biya ‘yan wasanta ya Fam miliyan £331, kuma matsakaicin dan wasa da ake biya duk mako shi ne Fam 54,000, sannan United ce ta hudu a biyan albashi mai tsoka tsakanin kungiyoyin Premier League, idan ka cire Manchester City da Chelsea da kuma Liberpool.
Manchester United tana ta takwas a teburin Premier League da maki 54, bayan cin wasa 16 aka doke ta 13 da canajaras shida sannan kungiyar ta ci kwallo 52 a Premier League a kakar nan, aka zura mata 55 a raga a babbar gasar firimiya ta Ingila.
Zuwa Kofin Zakarun turai
Yanzu dama biyu ta rage wa Manchester United, domin samun gurbin shiga gasar cin kofin Zakarun Turai ta 2024 zuwa 2025 amma duk da haka ba za ta buga kofin Zakarun Turai ba.
Gasar farko kenan da watakila da rarar kwallaye za a bi ta a raga, wadda ta taba yin haka a 1989 zuwa 1990, lokacin ta kare kakar a mataki na 13 a teburi kuma watakila kafin karshen wannan kakar ma kungiyar za ta iya yin kasa da haka.
Wannan shi ne karon farko da aka ci Manchester United wasa 13 a kaka daya a babbar gasar firimiya ta Ingila sai dai kociyan da suka ja ragamarta a kakar da ta yi rashin nasara 12 a 2013 zuwa 2014 da kuma kakar 2021 zuwa 2022.
To amma ta taba rashin nasara 16 a gasar rukunin farko a 1989 zuwa 1990, wadda ta karkare a mataki na 13 a teburin gasar amma a wannan kakar Manchester United an zura mata kwallaye 81 a dukkan karawar da take yi a bana, wadda aka taba durawa 81 a kakar wasa ta 1976 zuwa 1977.
Sauran wasa uku ya rage a gaban Manchester United, wadda za ta karbi bakuncin Arsenal ranar Lahadi, sannan ta kara da Newcastle United a Old Trafford a ranar Laraba. Ranar 19 ga watan Mayu, ne United za ta buga wasan karshe a bana a Premier League, wadda za ta je gidan Brighton kuma damar da ta rage a United domin kai wa gasar Zakarun Turai ta badi ita ce ta kammala kakar bana a mataki na shidan teburi, sai ta samu zuwa Europa Conference League.
 Haka kuma Manchester United za ta buga wasan karshe a FA Cup ranar 25 ga watan Mayu, idan ta dauki kofin zai ba ta damar shiga Europa League kai tsaye ta badi ko da a ce bata karkare a mataki na shida ba.
Shin Ya kamata A Kori Ten Hag?
Wasu suna ganin ya kamata shugabannin kungiyar su kori mai koyarwa Erik ten Hag saboda yadda yake jagorantar kungiyar akwai rashin kwarewa da kuma rashin salon buga wasa da ake bukata.
Amma kuma a duk lokacin da ya yi hira da manema labarai yana fakewa da cewa ‘yan wasan kungiyar suna yawan zuwa ciwo wanda hakan ne yasa baya samun cikakkun ‘yan wasan da za su bashi abin da yake so.
A wannan kakar kawai ‘yan wasan kungiyar sun samu Rauni kala-kala har sau 60, adadin da ba a taba samu ba a kan wata kungiya wanda hakan ya sa wasu suke ganin ba karamin kalubale bane ga shi mai koyarwa da ragowar masu taimaka masa da ma su kansu ‘yan wasan.
Sannan banda ciwo akwai matsaloli wadanda ba na cikin fili ba kamar rikicin shi kansa mai koyarwar da dan wasa Jadon Sancho da matsalar dan wasa Mason Greenwood da kuma matsalar nuna halin rashin da’a da dan wasa Marcus Rashford ya nuna a kwanakin baya.
A duk lokacin da aka yi masa tambaya a kan makomarsa, mai koyarwa Erik ten Hag yana cewa shi ne zai ci gaba da koyar da kungiyar har zuwa kakar wasa mai zuwa wanda hakan ba karamin kwarin gwiwa ya samu ba daga masu gudanarwa.
Sai dai duk da haka wasu suna ganin ba zai iya dawo da kungiyar hayyacinta ba domin bashi da kwarewar rike kungiya kamar Manchester United sannan suna ganin ya zama wajibi kungiyar ta shiga kasuwa domin neman masu koyarwa saboda ta maye gurbinsa.
Yanzu dai saura wasanni uku Manchester United ta kammala buga wasannin gasar firimiya inda za ta kece raini da Arsenal da Newcastle United da kuma kungiyar Brighton Albion sai kuma wasan karshe na gasar cin kofin kalubale na FA Cup da za su kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a ranar 25 ga wannan watan a filin wasa na Wembley dake Birnin London.