Tsohon Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ayyana yaƙi da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da suka addabi ƙasar nan.
Yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Irabor ya ce duk da tsananin matsalar tsaro a ƙasar nan, babu wata doka da ke nuna cewa Nijeriya tana yaƙi da ‘yan bindiga a hukumance.
- Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
- Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka
“Babu wata doka da ke nuna cewa Nijeriya tana yaƙi. Muna ɗaukar al’amari ne kawai kamar muna yin yaƙi,” in ji shi.
Ya bayyana cewa ayyana yaƙi a hukumance zai bai wa gwamnati damar haɗa dukkanin ƙarfinta da albarkatunta wajen yaƙar ta’addanci yadda ya kamata, tare da tabbatar da gaskiya da kulawa wajen kashe kuɗaɗen da suka shafi tsaro.
“Ayyana yaƙi zai taimaka wajen tsara albarkatun gwamnati yadda za a ga sakamako,” in ji shi.
Irabor ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ba ta hanyar amfani da sojoji kaɗai ba.
Ya ce ya kamata a samar da manufofi masu inganci da za su rage talauci, rashin aiki da yawan yara marasa zuwa makaranta.
“Idan muka rage yara marasa zuwa makaranta da kuma marasa aikin yi, za mu rage yawan mutanen da ‘yan ta’adda ke iya ɗauka aiki,” in ji shi.
Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina sa siyasa a batun harkar tsaro.
A ranar bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dakarun Nijeriya suna samun nasara a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, amma jam’iyyun adawa sun ce matsalar tsaro har yanzu babbar barazana ce ga ƙasar.