Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi kira ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya bar jihar ta zauna lafiya.
Fubara ya yi wannan kiran ne a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Mataimakiyar Gwamna Ta Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓe A Kagarko
- Sin Ta Bukaci A Yi Bincike Tare Da Hukunta Wadanda Suka Kai Wa Motocin Kamfanin Kasar Hari A Pakistan
Ya ce ba ya nadamar gudanar da zaben kananan hukumomi da aka yi a ranar Asabar da ta gabata duk da adawar da mutanen Wike a jam’iyyar PDP da APC suka yi.
Gwamnan ya bayyana cewa yana da karfin zuciyar daukar irin wannan mataki, kuma ya bukaci Wike ya daina tunanin yana wani iko a jihar.
Fubara ya ce ya yi duk abin da ya kamata don tabbatar da zaman lafiya a Jihar, ciki har da kiyaye duk wata yarjejeniya da suka yi da Wike, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya.
“Babu abin da ban yi ba don samun zaman lafiya. Zan iya fada muku sau nawa na durkusa na roƙi a bar wannan matsalar ta wuce. Na yi duk abin da zai yiwu,” in ji Fubara.
A lokacin da aka tambaye shi abin da zai ce wa Wike idan suka hadu, Fubara ya ce, “Zan fada masa cewa lokaci ya yi da zai kyale Ribas. Muna bukatar zaman lafiya.”