‘Yansanda sun kama Yusuf Haruna wanda aka fi sani da Lagwatsani, dan shekaru 18, da laifin kisan wani limamin Masallaci mai suna Sani Mohammed Shuaibu saboda ya hana su shan wiwi a kusa da Masallaci.
Yusuf ya daba wa limamin wuka lokacin da yake alwala, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya tabbatar wa da jama’a kudurin rundunar na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Gumel ya yi wa jama’ar jihar godiya kan irin goyon bayan da suke bai wa rundunar.
Ya kuma bukaci jama’a da suke kai rahoton faruwar laifuka ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen tabbatar da doka da oda a jihar.
Sannan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp