ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asalin Yadda Aka Samo Sunan Hausa Bakwai Da Banza Bakwai

by Mohammed Bala Garba, Maiduguri
2 years ago
Hausa

Wasu sun san garuruwan da ake kira ‘Hausa Bakwai’ da ‘Banza Bakwai’ amma ba su san dalilin da ya sa ake kiransu da wadannan sunayen ba.

Wannan ne ya sa naga dacewar yin wannan dan takaitaccen bayanin kamar yadda na taba karantawa a littafin ‘Kano Ta Dabo Cigari’ na Marigayi Wazirin Kano Alhaji Abubakar.

  • Ya Kashe Limami Saboda Ya Hana Su Shan Wiwi A Kusa Da Masallaci A Kano
  • Zargin Sata: Jami’an ‘Yansanda A Kaduna Sun Kama Buhunan Taki Guda 600

Bayan Bayajidda ya gudo daga Kasar Borno shi da matarsa mai suna Magaram saboda yunkurin kashe shi da Sarkin (Shehu) Borno ya yi, sai suka zo wani gari da ake kira Garun Gabas a ƙasar Hadeja. A nan ya bar matarsa saboda tsohon cikin da take dauke da shi ya wuce Daura. Bayan ya isa Daura cikin dare, ya sauka a gidan wata tsohuwa, sai ya nemi ruwa amma bai samu ba. Tsohuwar take faɗa masa dalilin da ya sa basa samun ruwa sai sau daya a sati saboda wata macijiya da take hana ɗibar ruwan. Da Bayajidda yaji haka, sai ya karɓi guga a wajen tsohuwar, ya nufi rijiyar Kusugu inda macijiyar take ciki, ya kashe ta ya ɗebi ruwa. Da gari ya waye, Sarauniya Kabara (wacce take mulkin Daura) ta ji labari, sai ta sa aka yi bincike aka gano Bayajidda ne ya kashe macijiyar. Ta kirasa ta ce za ta basa rabin mulkinta. Amma ya ƙi amincewa, ya ce mata sai dai a daura musu aure da ita idan ta amince. Sarauniya ta yarda, aka daura musu aure da Bayajidda. Sai jama’ar garin suka fara kiransa da ‘Makas-Sarki.’ Daga baya kuma suka koma ce masa ‘Sarki’ kawai. To daga nan ne aka samo kalmar Sarki da ake fadawa wasu sarakuna a yau. Da Sarauniya Kabara ta haifi da namiji, sai aka sanyawa yaron suna Bawo.

ADVERTISEMENT

A lokacin da Bawo yake mulkin Daura, an yi wata masifaffiyar yunwa a Kasar Hausa, wacce ta zama babu inda ake samun abincin mai yalwa sai a wani wuri wanda shi ne Kano a yanzu. Don haka kabilu suka riƙa ƙaura zuwa wurare masu ɗan yalwan abinci domin su tsira da rayuwarsu. Bayan jama’a sun fita kowa ya samu in da ya fake, sai ya zamana babu shugabanci kowa zaman kansa yake. Daga nan sai zalunci ya yawaita a tsakanin jama’a. Masu karfi su kwace kayan raunana. Wannan ne ya sa raunana suka fara kai kukansu Daura wajen Sarkin Bawo.

Da kararraki suka yawaita, sai Sarki Bawo ya yi shawarar kafa shuwagabanci a dukan wadannan wuraren da abin ya dama. Sai ya tura dansa Bagauda zuwa Kano, ya tura dansa Gunguma zuwa Zariya, ya tura ɗansa Duma zuwa Gobir, ya tura ɗansa Kumayo zuwa Katsina, ya bawa ɗansa Gazori riƙon Daura, ya bawa dansa Zamna Biram, ya tura dansa Kogo zuwa Rano. Wadannan garuruwa da Sarki Bawa ya bawa ‘ya’yansa ko ya tura su, su ake kiran Hausa Bakwai.

LABARAI MASU NASABA

Mummunan Zato

Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba

Akwai kuma Banza Bakwai, wanda Sarki Bawo ya sake tura wasu ‘ya’yan nasa bakwai zuwa can. Sai dai kuma wasu masana sun ce ba ‘ya’yansa na cikinsa ba ne, ‘ya’yan dan uwansa mai suna Karaf-da-gari ne wanda Bayajidda ya haifa da wata baiwarsa mai suna Bagwariya. Wadannan garuruwa bakwai da aka tura ‘ya’yan su ne: Zamfara da Gwari da Nupe da Yaruba (ilori) da Kwarrafa da Kebbi da Yawuri. Su ne ake kira Banza Bakwai.

Wannan shi ne asalin yadda aka samo sunan ‘Hausa Bakwai’ da kuma ‘Banza Bakwai’.

 

Mohammed Bala Garba, Maiduguri

Dalibi daga Jami’ar Tarayya ta Maiduguri (UNIMAID). 08098331260.

Hausa
Mohammed Bala Garba, Maiduguri
+ postsBio

    MASU ALAKA

    Mummunan Zato
    Muƙala

    Mummunan Zato

    November 23, 2025
    Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba
    Muƙala

    Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba

    June 30, 2025
    Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya
    Muƙala

    Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya

    December 3, 2024
    Next Post
    Mutane 19,000 Sun Amfana Da Tallafin Fadama III A Zamfara

    Mutane 19,000 Sun Amfana Da Tallafin Fadama III A Zamfara

    LABARAI MASU NASABA

    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

    June 24, 2026
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

    June 24, 2026
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

    June 24, 2026
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

    June 24, 2026
    Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

    Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

    June 24, 2026
    Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

    Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

    June 24, 2026
    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

    June 24, 2026
    Sabbin Ministoci

    Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

    June 24, 2026
    Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

    Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

    June 24, 2026
    Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

    Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

    June 24, 2026

    © 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

    No Result
    View All Result
    • Gida
    • Labarai
      • Manyan Labarai
      • Kananan Labarai
      • Masarautu
      • Bakon Marubuci
      • Dausayin Musulunci
      • Daga Kasar Sin
      • Nishadi
      • Noma Da Kiwo
      • Sana’a Sa’a
      • Tambarin Dimokuradiyya
      • Taskira
      • Daga Birnin Sin
      • Ado Da Kwalliya
    • Siyasa
    • Wasanni
    • Al’adu
    • Al’ajabi
    • Labaran Kasuwanci
    • Karanta cikin Turanci

    © 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.