Wani matashi mai suna, Chukwudi Ugwu dan shekaru 25 a duniya, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Ibadan a Jihar Oyo, bisa zarginsa da satar akuya da babur a barikin ‘yansanda.Â
Mai gabatar da kara, DSP Adewale Amos, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar da wasu da suka tsere a ranar 3 ga watan Afrilu, a barikin ‘yansanda na Iyaganku da ke Ibadan, sun hada baki wajen satar akuyar da kudinta ya Naira 250,000 ta wani mutum mai suna Olawole Oke.
- Sanata Barau Jibrin Ya Ƙaddamar Da Motocin Zirga-Zirga A Kano
- Liverpool Ta Bayyana Arne Slot A Matsayin Wanda Zai Maye Gurbin Klopp
Ya kuma yi zargin cewa wanda ake karar da sauran a ranar sun sace wani babur kirar Bajaj da kudinsa ya kai Naira 250,000 mallakin wani David Adepoju kuma laifin ya saba da sashe na 516 da 390 (9) na dokokin laifuka na Jihar Oyo na shekarar 2000.
Alkalin kotun, Mista Maruff Mudashiru, ya bayar da belin wanda ake karar kan kudi Naira 200,000 sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Yuli.