Kamar dai yadda masana kan ce duniya gida ne guda ga daukacin bil adama, ta yadda abun da ya samu wani bangare na duniya na iya yin tasiri zuwa ga sauran sassan ta, haka abun yake game da batun sauyin yanayi. Mun dai ga yadda a shekarun baya bayan nan tasirin sauyin yanayi ke haifar da bala’u iri daban daban a bangarorin duniya mabanbanta.
Sassan kasashe daban daban na fuskantar ibtila’in fari, da ambaliyar ruwa, da kwararar hamada, da matukar karuwar zafi irin wanda kan hallaka nau’o’in halittu daban daban dake rayuwa a doron wannan duniya.
A cewar masana, watan da ya gabata, ya kasance Agusta mafi zafi, da masu binciken kimiyya suka tantance ta amfani da na’u’rorin zamanin yau, kuma watan Yulin da ya gaba ne kadai ya fi shi zafi bisa alkaluman da aka tattara.
Bisa wannan sakamako ne ma babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa, yanayin duniyar mu na kara tabarbarewa, inda a bana duniya ta yi fama da garjin-rana mai matukar kuna, wanda ya zamo mafi zafi a tarihi.
A bangaren masana, dake ba da shawarar hanyoyin tunkarar wannan kalubale kuwa, da yawa na cewa tuni lokaci ya yi na daukar matakai tare, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. Wannan shawara na nufin jagorori a matakai daban daban, su zabura wajen aiwatar da matakan gaggawa bisa hadin gwiwa, domin yayyafawa wannan matsala ruwa.
A halin da ake ciki yanzu, duniya ba ta da lokacin jira, ko na batawa. Don haka muna iya cewa, matakan tarukan kasa da kasa, kamar taron sauyin yanayi na MDD wanda za a gudanar a karshen watan nan na Satumba a birnin New York, da taron COP28 na watan Nuwamba a hadaddiyar daular larabawa, da ma wanda ya gudana a Kenya a baya bayan nan da makamantan su, sun zo a kan gaba. To sai dai kuma, duniya ta fi bukatar matakai na zahiri na cimma wannan buri, irin su cika alkawuran da manyan kasashen duniya suka jima suna yi, na samar da kudade, da kwarewar makamar aiki, da hadin gwiwa kai tsaye tare da kasashe masu rauni da masu tasowa, ta yadda za a kai ga cin gajiyar matakan kimiyya da fasahohin zamani, na shawo kan sauyin yanayin nan dake addabar dukkanin duniya baki daya.
.