• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Wajaba Amurka Ta Kaucewa Sake Maimaita Irin Kuskuren Da Ta Aikata Game Da Taiwan

byCMG Hausa
3 years ago
Amurka

A duniyar yau, ba wanda ya zarce Amurka a fannin iya maida fari baki, da juyar da tunanin al’umma.

Kasa ce dake kan gaba wajen ta da husuma, da kin karbar kuskuren ta, da sauya matsaya da cin dunduniya, halayen da suka zamewa kasar dabi’a a duk lokacin da take cudanya da sassan kasa da kasa.

  • Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan

To sai dai kuma, karya ba za ta tserewa gaskiya ba. Idan an kalli batun da ya shafi takaddamar zirin Taiwan, duk mai hankali zai fahimci abu ne da Amurka ta tsara domin yin tsokana.

Bisa nufinta na tabbatar da daidaito a zirin Taiwan, tun da wuri Sin ta bayyana rashin amincewa, da shirin ziyarar kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi, kasar Sin ta yi ta nanata mummunar illar da ziyarar ta Pelosi za ta haifar, da ma sakamakon da Amurkar za ta samu idan har Pelosi ta aiwatar da ziyarar, duk da kashedin da ya fito daga sassa daban daban.

Dokokin kasa da kasa, sun baiwa kasashe ikon mulkin kai da tsaron yankuna, kana sun haramtawa duk wata kasa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wata. Don haka, bisa kunnen kashe da Amurka ta yi, ta aikata mummunar ta’asa, kuma Sin ba ta da zabi, illa ta mayar da martani.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Matakai daban daban da kasar Sin ta aiwatar domin mayar da martani ga waccan ziyara, na da nufin yin gargadi ne ga masu aikata ta’asa, ta yunkurin samar da ’yancin Taiwan.

Sin ta zartas da matakan kare babbar moriyarta bisa doka. Kuma matakan nata sun dace da dokokin kasa da kasa da na cikin gida.

Tun fil azal, yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin. Kuma sakamakon tsokana daga waje, ya sa dakarun sojin kasar Sin suka gudanar da atisayen soji, da sarrafa makamai a yankunan tekun dake daura da tsibirin na Taiwan, a wani mataki na tabbatar da ikon mulkin kai, da tsaron yankunan Sin. Wannan kuma na kunshe ne cikin tanade-tanaden kundin mulkin kasar, da dokokin dake haramta yunkurin ballewa daga kasar, da ma sauran dokoki masu nasaba da hakan.

Manufar kasar Sin daya tak a duniya, muhimmiyar ka’ida ce da kasar Sin ke karewa. Don haka ya wajaba, Amurka ta koyi darasi daga matakin kuskure da Pelosi ta aikata, ta komawa hanya madaidaiciya, wadda za ta dace da manufar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyi 3 da sassan biyu suka sanyawa hannu.

Ya wajaba Amurka ta kaucewa kara yin wasu kura-kurai. Idan kuma ta ci gaba, Sin za ta maida martani yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Hukumar NDLEA Ta Cafke Wani Basarake Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Sakkwato

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version