Kamar yadda ta saba a kowace shekara, a bana ma Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group bisa jagorancin Shehu Isma’ila Umar Almadda ta cika makil babu masaka tsinke a ranar Asabar da ta gabata domin raya daren Maulidin Manzon Allah ((SAW)) na bana, a Layin Matazu Close da ke kusa da Titin Kagoro, a Unguwar Sabon Garin Tudun Wadan Kaduna.
Maulidin wanda aka gudanar daga karfe 8 na dare zuwa wayewar garin Lahadi, 12 ga Rabi’ul Auwal 1446BH, ya kuma kunshi yaye wata daliba, Sa’adatu Isma’ila Umar da ta haddace Alkur’ani mai girma da kuma wasu dalibai biyu, Sayyada Aisha da Abdulrahman, wadanda suka yi sauka kuma suka fara haddace fiye da izu 20.
- Zaben Gwamna: Kallo Ya Koma Jihar Edo
- An Gudanar Da Bikin “A Rubuce A Sama: Labarina Na Kasar Sin” Don Murnar Cika 75 Da Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin A Abuja
Duk da mamakon ruwan sama da aka yi ta kwararawa a daren Maulidin, Shehu Isma’ila Umar Almadda tare da mahalarta sun jajirce wajen raya daren har zuwa wayewar gari bayan ruwan ya dan sarara.
Da yake tattaunawa da manema labarai kafin fara zaman Maulidin, Shehu Isma’ila Mai Diwani ya bayyana Manzon Allah ((SAW)) a matsayin wanda ya kawo wayewa ta karshe ga duniya.
“Mun gode Allah da ya nuna mana ganin wannan rana ta haihuwar manzon Allah (SAW) wanda samunsa, Ubangijinmu ya gaya mana “bai aiko shi ba sai don ya zama Rahma ga halitta duk gaba daya”, shi jin kai ne kuma Rahma ne ga halitta, samun wannan Rahma, shi ya sa muke wannan murna. Duk wanda ya san wannan Rahma ya san ta shafe shi, duk haliita kuwa, ta shafe su, bare mabiya addininsa, ta shafe su a bisa kebance.
“Kadan daga cikin abubuwan da zaman Mauludi ke samarwa: Alkur’ani ya gaya mana cewa, Annabi Muhammad (SAW) Rahma ne ga Halitta duk baki daya. Hadisi ya gaya mana, Annabi (SAW) shi ne mai ceton halitta a ranar Alkiyama, kuma shi ne shugaban duk dan Adam. Tun daga kan Annabi Adam har kan karshen ‘ya’yansa (Mursalai, da Annabawa da waliyyai da shugabanni da sauran al’umma) duk suna karkashin tutar Manzon Allah (SAW) a ranar Alkiyama.
“Annabi Muhammad (SAW), shi ne cikamakon Annabawa, shi ne jagoransu kuma limaminsu. Duk wata wayewa, ko duk wani abu da wani ma’aiki zai zo da shi, Annabi (SAW) ya zo da karshensa, sai dai malamai su yi ta warwarewa kuma har kiyama ba za su gama ba. Don haka, babu bukatar wani Annabi ya zo da wani abu sabo, sai dai a warware wata fahimta da Annabi (SAW) ya zo da ita.
“Addinin Annabi Muhammad (SAW), shi ne mafificin addinatai, kowanne addini ya yi rawar gani cikin wayewar tunanin dan Adam, tun daga kan Annabi Adam (AS). Dan Adam wuta ya fara gani, tun yana tsoronta har ya iya sarrafa ta, zai iya gasa nama ya ci, ba kamar dabba ba da ke cin nama danye. Dan Adam ya ci gaba da wayewa, har yanzu, ta kai dan Adam fannin iya girke-girke. Dan Adam, tun a zamanin Annabi Adam ya koya yadda ake birne gawa, ba kamar dabba ba da za a jefar. A wancan zamani, fahimtar karama ce, kalmomin zance, ba su da yawa, kuma Uwa ce shugaba, ana danganta ‘ya’ya ga iyaye mata saboda sukan rika zuwa wurin Maza daban-daban.
“A zamanin Annabi Nuhu, dan Adam ya kara wayewa, ya fahimci akwai Uba Namiji. Daga nan, dan Adam ya koyi kira, har ya iya hada jirgin da zai tsira da shi a cikin ruwa. A zamanin Annabi Idris, dan Adam ya fara koyon haruffan rubutu, ta yadda zai tura sako a rubuce. A wannan zamani dan Adam ya fara dinkin kayan rufe Sutura wanda a baya yake amfani da ganye.
“Dan adam ya ci gaba da wayewa har ya fara gina dakin Ibada. Yana daga cikin wayewa ta Annabi Ibrahim (AS) hana layya da dan Adam sai dai a yi da dabba, tun daga zamanin Annabi Ibrahim (AS), dan Adam ya tsira daga yankawa don Ibada, sai dai a yanka Dabba. Hakan, sai ya tabbatar da Ma’anar ayar “Wa man DakHalahu kana amina” duk wanda ya shiga Makkah, ta zama aminci a gare shi, kar ya yi fargabar za a yi hadaya da shi sai dai a fanshe shi da dabba.
“Annabi Ibrahim (AS), shi ya zo da wayewar a hadu a Ubangiji daya, maimaikon kowa ya yi nashi. Shi ya zo da wayewar komai na iya canzawa sai dai Allah.
“Annabi Yunusa ya taka rawar gani wajen wayewar dan Adam, a zamaninsa aka daina auratayya a tsakanin ‘yan uwa na jini, sabanin Shari’ar Annabawan da suka gabata. Daga nan, dan Adam ya ci gaba da wayewa, zamani bayan zamani har Annabi (SAW) ya zo da karshen wayewa, ya tarar dan Adam ya iya karatu da rubutu da Addini, daga nan ya ci gaba, har zuwa wannan zamanin Kimiyya da fasaha da muke kai ya samu. Babbar fasaha, wayar Salula – ta kwace littattafai, da Rediyo da Talabijin duk suna cikinta, ta tattare duniya baki daya. Wannan duk suna daga cikin abin da Ubangiji ya fada wa ma’aikinsa Annabi (SAW).
“A’ummar Annabi (SAW), ita ce mafificiyar al’umma, ta wajen ci gaba, addini da komai ma baki daya. Haka kuma, littafinsa, shi ne mafificin littattafai. Ilimin da ke tattare a cikin littafin, akwai Hadisin da ya ce, ‘sai dai Malami ya gaji, amma ba zai taba cewa, ya kai makura ba a Alkur’ani. Muhyiddinil Arabi, ya tafi cewa, duk wata aya ta Kur’ani kanun wani fanni ne na Ilimi, Shehu Ibrahim Inyass ya tabbatar da wannan ikirarin. Shehu ya fitar da fannin Ilimi 10 a aya daya tak ta Alkur’ani, sannan a Suratul Fatiha, ya fitar da fannin Ilimi 9 a cikinta.
“Manzon Allah (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya fito a ranar tashin Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, yana da tsani wanda in an hau, za a samu tsira a ranar tashin Alkiyama, Ubangiji ya girmama shi da abin da bai girmama waninshi ba, Allah ya daukaka ambatonsa, ya gafarta masa, ya tafiyar da dauda ga ‘ya’yan gidansa, ya yi Isra’I da shi, ya yi rantsuwa da shi, ya yi rantsuws da zamaninsa, da garin da aka haife shi, ya ba shi Alkausara (Alkairai masu yawa). Annabi (SAW) kadai Allah ya kebanta da wannan, duk in zamaninsa ya yi nisa, girmansa sake bayyana yake yi, amma sauran Annabawa, sai dai a jingine maganganunsu.
“Akwai wani Fitaccen malami, Moris da ya kamanta Fasahar Zamani a kan maganganun Alkur’ani da Littafin kiristanci (Bible) da Yahudanci, abin mamaki, sai ya ce, suna cewa, Alkur’ani ba maganar Allah ba ce, amma shi ne ya tafi da zamani.
“Zamani yana kara nisa, Mu’ujizarsa ((SAW)) tana kara fitowa, amma sauran Annabawa, zamani yana kara nisa, Mu’ujizarsu tana shudewa.
“Annabi (SAW), Allah ya aiko shi ga duk Duniya, Annabin Amurkawa, Sinawa, Rashawa, Larabawa, Afirkawa da duk duniya. Don haka, wani karatun a matsayinka na wani dan yare, in bai maka dadi ba sai ka ga wani Yare ya yi masa daidai.
“Wannan zama na tuna rayuwar Annabi Muhammad (SAW), makaranta ce da take karantar da mu abubuwa masu yawa na daga dabi’u da koyi da Annabi (SAW). Yana daga cikin abin da wannan zama ke koyarwa, Soyayya ta duk inda ta zo na daga rabe-rabenta.
“Soyayyar wajibi: Soyayyar Ubangiji da ma’aikinsa, da Littafinsa (Alkur’ani), in ka yarda kana da Ubangiji, ya zama dole ka so shi, ita kuma soyayyar Ubangiji dole sai ta hadu da ta ma’aikinsa da littafinsa. Yaya ake soyayyar Ubangiji da ma’aikinsa? Dole sai an koya! Wannan zama yana koyar da irin wannan soyayya.
“Soyayyar Girmamawa: soyayyar iyaye, mu yi musu alkairi, mu tuna wahalar da suka yi da mu, sai mu girmama su. Soyayyar Malami: Dole ne ka girmama Malaminka wanda ya sanar da kai Ilimi, da wanda ya taimake ka a rayuwa. Soyayyar tausayi: soyayyar ‘ya’ya, da ‘yan uwa, da Almajirai, da Abokai. Soyayyar Sha’awa: Soyayyar Iyalinmu, Gine-gine, Dukiya, Abinci, Noma, Kasuwanci da sauransu.
“Wannan idan mun lura, mauludi duk yana koya mana haka, saboda mun yi Ado, mun yi Girke-girke, mun yi abubuwa da yawa tare da iyayenmu, da abokanmu, da ‘yan uwanmu da almajiranmu da mataimakanmu, duk za ka ga irin wannan soyayyar gaba daya ta bayyana a yau (ranar mauludin).
“Wannan zama yana koya mana koyi da wanda ake yin zaman don shi (Annabi Muhammad (SAW), mu zama cikin mabiyansa kuma masoyansa masu lafiyar zuciya. Kar ka zama daga cikin masu yajin zuciya – komai ya zama fada, mu zama masu yalwar zuciya wajen zaman tare, mutunta juna, mutunta Addinatai ga kowa, kar ka zagi addinin kowa, kar ka bata nasa, sai fitina ta afku! Ubangiji cewa ya yi, zai yi mana hukunci, don haka, hukunci na hannunsa ba a hannunmu ba.
“Wannan zama yana koya mana mutunta al’adar kowa, mutunta wurin Ibadar kowa, da mutunta fahimtar kowa, da girmama abin girmamawar wasu kamar Bukukuwan Mauludi.
“Akwai hujjoji daga Allah, babu wanda zai ce ya fi masu mauludi hujja sai dai ya fi su bakin zagi ko rashin kunya amma in dai dalili ne an fi shi. “Ina karanta maka labarun Annabawa don zuciyarka ta nutsu”, duk fadin zuciyar Annabi Muhammad (SAW), amma Ubangiji ya ce masa, yana ba shi labaran sauran Annabawa don zuciyarsa ta nutsu. In dai, labaran Annabawa ya nutsar da zuciyar manzon Allah (SAW), mu ina zuciyarmu? To mu kuma, ga labaran Annabi (SAW), ta ina za muje ga labaran wasu Annabawa?
“Malaman Hadisi sun ce, sun dauki Mauludi a cikin Azumin Ashura na Annabi (SAW) da ya rika yi, da kuma Rago da ya yanka wa kansa duk da ya san Baffansa, Abdulmuddalibi ya yi masa Akika, kuma a Shari’arsa ba a yin Akika sau biyu da sauran abubuwan da ke nuna murnar haihuwarsa.
“Alhamdulillah, yanzu a wayewarmu, muna da wani abu da muka rike, kar saboda kai ba ta yi maka ba, ka wulakanta mana abin da muke so. Hakan na daga cikin abinda ke kawo fitina saboda rashin wayewa. In ba ka fahimci abu ba, sai ka tattauna da masu abin da niyyar fahimta ba don wulakantawa ba.
“Ana ba da wani labari, wasu waliyyan ma’aurata ne suka tafi sulhun aure, bayan dawowarsu sai suka bayar da rahoton cewa, aure ya mutu, sai aka ce musu, dama ba ku tafi da niyyar sulhu ba sai dai don rabuwa, saboda Ubangiji ya ce, “in kuna da nufin yin Sulhu, Allah zai datar da ku”.
“Don haka, wanda ya zo yana nufin fahimtar wani abu da bai sani ba, Allah zai datar da shi. Musamman ta hanyar tattaunawa mai kyau a tsakanin masana ba tsakanin jahilai ba. Haka nan, wannan zama yana koyar da mu cewa, Musulunci yana tafiya da birni tare da Ilimai, Fannoni, Ladabai, Noma, Gine-gine, Tattalin arziki, Zamantakewa, Adabi, da Al’adu.
Wannan zama yana koya mana yadda kyakkyawan aiki zai fi surutunmu yawa. Haka kuma, zaman zai koya mana karantar da musulmai kame kai, da hakuri, da yalwar zuciya. Saboda fadarsa ma’aikin Allah (SAW), “Ku rika yin Bushara ba korewa ba, ku rika sassautawa ba tsanantawa ba, ku rika cewa an yi daidai amma dan kara kusantowa”. Ya bayyana.
A halin da ake ciki kuma, Shehu Isma’ila Umar Almadda, Shehin Malamin, ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ta raba su da muhallansu da ahlinsu, musamman mutanen Maiduguri Jihar Borno da madatsar ruwa ta Alau ta balle, ruwa ya kwaranyo cikin gari ya mamaye fiye da rabin birnin. Allah ya sa hakan ya zama wani budi da zai haifar da alkairai a cikin garin.
Ya yi kira ga gwamnati, da ta kara kaimi wajen ganin irin hakan bata sake faruwa ba a nan gaba. Ya kara da cewa, “idan gwamnati ta yi wa ‘yan kasarta abu mai kyau ba sai ta fito yakin neman zabe ba, ‘yan kasa sun san an yi musu abu mai kyau kuma za su so abin ya ci gaba da gudana.
Sannan ya sake kira ga gwamnati da ta kara duba dabarunta kan yaki da matsalar tsaro. Inda kuma ya yi kira ga ‘yan kasa, da su ci gaba da godiya ga Ubangiji kan duk irin halin da suka tsintsi kansu, duba da yadda wasu kasashe ke cikin mawuyacin hali fiye da mu.
Shehu Mai Diwani, ya bukaci ‘yan kasa, su rika yi wa shugabanni Addu’a, “kana mu rungumi karatu, da sana’o’i sannan mu dogara ga Allah. Albarkar Annabi (SAW), albarkar irin wannan zama da muke yi, Allah zai ba wa kasarmu lafiya da abin da lafiya za ta ci. Allah ya rike hannun shugabanni domin kai kasa gaci. Allah ya ba wa kasarmu lafiya!”
Ya kuma gode wa ‘yan jarida wadanda su ne kashin bayan halitta, masu wayar da kan al’umma. Daga cikin ‘yan jaridar da suka halarci zaman Mauludin sun hada da Jaridar LEADERSHIP, Gidan talabijin na AIT, Gidan Rediyo da talabijin na KSMC, Gidan talabijin na Trust Tb, Gidan Talabijin na DITB, Gidan Rediyon Nijeriya Kaduna (FRCN), da sauransu.