• English
  • Business News
Friday, September 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

Sheikh Isma’ila Almadda Ya Bukaci Malamai Su Rungumi Fahimtar Addini Bisa Sauyin Zamani

by Sulaiman
19 seconds ago
in Rahotonni, Manyan Labarai
0
Ahlul Faidhati Mai Diwani Group

HOTO: ranar Maulidin fiyayyen halitta a Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Kaduna, 4 Sept., 2025

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Hani’an Li Ibrahima laha hilaluhu, hilalun bada linnazirina jamaluhu.

 

Bayan gaisuwa da yabo ga kafafen yada labarai, Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) ya fara gabatar da jawabi dan gane da abinda ya tattaro al’umma daga sassa daban-daban na Nijeriya da ketare a Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Kaduna.

 

Taron Maulidin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW wanda aka saba gudanarwa duk shekarar a Zawiyar ta Mai Diwani Kaduna, a bana ta zo da sabon salo domin Annabi SAW ya cika shekara 1,500 da haihuwa wannan abu ne mai girma kwarai da gaske.

Labarai Masu Nasaba

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya

 

Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu. Ubangiji tabaraka wata’ala ya yi murnar ranar haihuwar Annabi Yahya AS (wasalamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare shi (Yahya), ranar da aka haifeshi, da ranar da zai koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe shi da rai). Annabi Isa AS kuwa, da kanshi ya yi murnar ranar haihuwar shi, (wasalamun alayya yauma wulittu wa yauma amutu wa yauma ub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare ni, ranar da aka haife ni da ranar da zan koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe ni da rayuwa). Annabi SA da kansa ya yi murnar ranar hauhawar, a yayin da aka tambaye shi game da Azumin Litinin da yake yi, sai ya ce, (Zaka yauma wulittu fihi – wannan itace ranar da aka haife ni), don haka komai na Annabi SAW ke zuwa ranar Litinin: haihuwa, Hijira da rasuwa duk Litinin, sabida muhimmncin wannan rana.

 

Wannan shi ne abinda ya tara mu a wannan rana ta Maulidin cikar Annabi SAW shekara 1,500 da haihuwa, wannan murna ce kan murna.

 

Duk wanda yake shekara 30 da haihuwa a yanzu (2025), ya ga lokacin da duniya ta yi bikin cikar Annabi isa AS shekara 2,000 da haihuwa a shekarar 2000, Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da manyan kasashen duniya sun yi murnar wannan rana har da kasashen Musulmi saboda Annabi Isah na kowa ne, to me zai hana Musulmin duniya murnar bikin cikar Annabi SAW shekara 1,500 da haihuwa ba? Kuma Allah ya sa mun ga wannan rana, tun da mun zo a wannan zamani, kuma ba za muga shekarar da Annabi SAW zai cika 2,000 da haihuwa ba sai dai jikokin jikoki, mu kuma mun zama mutanen da, sai kaji suna cewa, kakanninmu sun ga zamanin da Annabi SAW ya cika shekara 1,500 da haihuwa. Da wannan muke cewa, za a kai lokacin da jikoki za su yi murna kakannin su sun ga wannan rana ta 1,500 kuma sun yi murna da ita. Kamar yadda na baya suka yi murna da cikar Annabi 1,000 har zuwa 500 (karewar Daular Abbasawa) har zuwa kan sahabbai da suka yi zamani da Annabi SAW.

 

Dangane da sabanin fahimta da ke dabaibaye da batun Maulidin Annabi SAW, Shehu Almadda ya yi karin haske da cewa, kowane dan Adam yana nan rike da tarihin kakanninsa da iyayensa, don haka, yana daga cikin sakaci da aka tusawa samari a wannan zamani, rashin girmama tarihin Annabinsu. Abin takaici, kaga mutum yana kiyaye tarihin shugabansa na siyasa, makaranta, wurin sana’a amma Annabinsa ko oho!!! Kowace al’umma tana alfahari da Annabinta, amma sai mu Al’ummar Annabi ne kadai za mu ce ba haka ba. Girmama Annabi shi ne girmama Addininsa, girmama addinninsa shi ne girmama kanmu. Rashin girmama Annabi shi ya jawo rashin girmama addini, shi ya jawo rashin girmama kanmu, kuma shi ya jawo duk abinda ke faruwa yanzu ke faruwa.

 

Annabi Muhammad SAW, mahaifinsa Abdullahi da mahaifiyarsa Aminatu, an haife shi a Makkah, sai da ya cika shekara 40, sannan Allah ya aiko shi don ya isar da sakonsa tabaraka wata’ala. Shi yafi kowa sanin Allah, shi ya gaya mana akwai Allah, mu kadai ta shi, Allah ya hado shi da Alkur’ani wanda ya tattaro mana duk hukunce-hukuncesa aciki. Annabi SAW ya yi zaman Annabta har na tsawon shekara 13 a Makkah sannan ya yi Hijira zuwa Madina ya yi shekaru 10 sannan ya koma ga Ubangiji. Bayan rasuwar Annabi SAW, sahabbai sun fara kirgar Kalenda da Hijira, yau Hijira 1447, in muka hada ta da shekarun Annabi SAW (40 + 13 + 10 + 1447 = 1,500).

 

Alkur’ani kuma zai cika shekara 1,500 da saukarwa nan da shekaru 40 masu zuwa. Wannan ba karamin alkairi ba ne, don haka muke Azumin watan Ramadan. Kowane littafi, yana samun girma ne da girman wanda aka saukar mawa, don haka, Littafin da aka saukarwa Annabi Muhammad SAW, ya fi dukkan Littattafan da aka saukarwa Annabawa. Kuma littafin ya yi daidai da kowane zamani, don haka, ake kiran Malamai masu fassara Alkur’ani da su rika fassara shi da irin fahimtar zamaninsu, wayewar zamani da irin ilimin zamani (kimiyya da fasaha).

 

Duk ilimi, yana karkashin kayayyakin da ake yin sanin da shi, misali, karfin gani na Ido, ba zai yi daidai da yadda dattijo yake gani ba da yadda saurayi ke gani, har ya zama dattijo ya daina gani amma Alhamdulillah, a wannan, zamani sai kwararrun malamai suka kirkiro medikal glass, wanda dattijo zai iya amfani da shi, karfin ganinsa ya zama kamar wani dan saurayi. Da yawan Malamai an yi fatawar a daina amfani da karatunsu a lokacin da suka tsufa sabida ba sa iya ganin littafinsu, da akwai glass na ido a wancan lokaci da ba a yi musu wannan fatawa ba. Bayan Medikal glass na gani akwai wanda yafi shi karfi na binciken kwayoyin halitta (microscope), sannan akwai kuma na hangen sararin samaniya da NATA ke amfani da shi (Telescope). Ma’ana kowane kayan Ilimi akwai inda ya dace da shi.

 

Malamai suna fassara ‘Jifanin kal jawabi, wa kudurir rasiyat’ da cewa manyan farantai na cin abincin rundunar yaki, amma a wannan zamani, Malamai suka ce a’a, (Satelite signal ne da tukwanen Nukiliya) Allah ke nufi, kuma saboda irin wannan fasaha ta Annabi Sulaiman ce ta janyo sarauniya Balkisu ta musulunta a lokacin da ta shiga masarautar shi har ta dimauta saboda ganin fasahohi.

 

 

Wani masani, Morris Bukay a wuraren 1960, ya bayyana cewa, Alkur’ani ya fi karfin ilimin Larabawa, ya fi karfin ilimin zamanin da ya sauka da wanda ya zo bayansa, kuma ya fi karfin ilimin na turawa na wannan karni na 19 kuma ya fi karfin ilimin zamanin da zai zo nan gaba. Saboda wannan yabo, Sarki Faisal ya yi masa kyauta.  Morris Bukay, shi ya yi littafin fassarar Alkur’ani inda ya kwatanta Ilimin Alkur’ani da fasaha da Injila (Bible) acikin littafinsa mai suna “The Bible, the kur’an, and Science”.

 

Har ila yau, dangane da makasudin taron, Almadda ya yi karin haske da cewa, batun Maulidi Haram ne ko ya inganta ko bai inganta ba, DAkIkANCI ne, an wuce wannan zamani, a yanzu batun tarihi ake yi na tina ‘yan mazan jiya a zamanance, a duniyance, a ilimance haka kuma a lahirance. Duk 1 ga Oktoba, Nijeriya tana murnar ranar ‘yancin kai, muna taya wadanda suka samo mana ‘yancin kai don mu rike kasarmu da kyau. Haka kowane gwarzon namiji, in ranar haihuwarsa ta zagayo, yakan tara ‘yan uwa da abokan arziki da yaransa don tayasa murna. Haka yake a kowace kasa, hatta Saudiyya tana murnar ranar ‘yancin kai da suke jira “janadariyya”, sarakunanta da ganguna rike da takubbuna domin ranar ‘yancin kai amma ai yafi da cewa, su yi murnar ranar da Annabi SAW ya ‘yantar da Makkah daga Gumakan da ke cikin Ka’aba.

Don haka, kowa ya rike wannan, a tarihi BA HARAM ko HALAL sai dai GASKIYA ko kARYA, misali, Annabi Muhammad SAW an yi shi har ya zauna a Makkah da Madina ga hujjoji ko kuma wani ya ce, karya ne, mun je mun yi bincike babu wannan lamari. To mu fahimci wannan taro, tarihin Annabi SAW, Allah ya yi mana tarihin Annabawa da yawa a Alkur’ani, ya yi mana tarihin dan Adam, ya dace al’umma ta waye, batun tarihi babu batun Bid’a ko haram sai dai GASKIYA ne tarihin ko kuma akasin haka.

 

Daga karshe, Mai Diwani ya yi kira ga sauran Malamai shugabannin al’umma da cewa, su yi koyi da zaman Annabi SAW a Madina (Birni), me yasa ya sanya mata Birni bai ce garin Musulmai ba? Saboda birni, shi ne mai sauyawa, bai tsayawa akan abinda ake cewa, “na mu ne, ko kuma haka muka gada” (kauye). Allah ya yi alkawarin halakar da kauye, ma’ana, wanda bai sauyawa, wata rana sai an nemi abin an rasa. Don haka, Annabi SAW ya fita daga Ummul kura (Makkah) saboda babu yadda za a yi  a canzata, dakin kakanni ne, ba zaka zo da sabo ba wanda ba nasu ba, ya tafi Madina inda ya kafa kundin tsarin mulki na farko mai suna “wasikatu Madina”, duk wanda yake Madina, dan kasa ne a zauna tare a kiyaye kasa tare kuma a gudu tare, ya yarda Yahudawa, Nasara, Munafikai da wadanda ba za su bi shi ba duk a zauna wuri daya a zauna lafiya, duk abunda ya faru, warware tsarin kundin mulki ne ya jawo Annabi SAW ya hukunta su.

 

Annabi SAW ya fada cewa, duk in addininsa ya cika shekara 100, Allah zai kawo wani ya sabunta shi saboda ya tsufa, fahimtarsa ta tsufa, a nan zamu fahimci cewa, in har duk bayan shekara 100 Allah zai tura wani ya sabunta addini, yau Addininmu yana kan shekara 1447, don haka, ya zama dole Malamai su waye.

 

Sannan ya yi kira ga ‘yan kasa, su amsa kiran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wurin yin katin zabe domin kowa ya zabi ra’ayinsa kuma ‘yancinsa ne domin shi dan kasa ne.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

Related

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur
Manyan Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

12 minutes ago
Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya
Manyan Labarai

Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya

1 hour ago
Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL
Manyan Labarai

Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL

3 hours ago
Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
Manyan Labarai

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi

4 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

20 hours ago
DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci
Manyan Labarai

DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

1 day ago

LABARAI MASU NASABA

Ahlul Faidhati Mai Diwani Group

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

September 12, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

September 12, 2025
Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya

Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya

September 12, 2025
Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

September 12, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

September 12, 2025
Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL

Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL

September 12, 2025
Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi

September 12, 2025
Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi

Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi

September 12, 2025
Buƙatar Daƙile Yawan Ɓacewar Mutane A Nijeriya

Buƙatar Daƙile Yawan Ɓacewar Mutane A Nijeriya

September 12, 2025
Tattalin Arzikin Sin Babban Ginshiki Ne Na Karuwar Tattalin Arzikin Duniya

Tattalin Arzikin Sin Babban Ginshiki Ne Na Karuwar Tattalin Arzikin Duniya

September 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.