Da sanyin safiya, mata sanye da bakaken kaya da maza a cikin bacin rai sun hallara a makabartar Sayyida Nafisa da ke birnin Alkahira wadda dadaddiyar makabarta ce da aka assasa shekaru aru-aru da suka gabata.
Amma ba sun zo ne domin binne danginsu ba. Sun zo ne domin su tone gawarwakinsu.
- Mace Aba Ce Mai Daraja, Ba Sai Ta Ba Da Kanta Ba Za Ta Yi Suna A Fim – Jamila Saleh
- Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda
“Abin na da tayar da hankali matuka,” in ji Iman yayin da take kuka da kuma jagorantar tono gawarwaki.
“Na farko mahaifiyata mai bani shawara, ta rasu shekaran jiya. Yanzu ina tono gawarta da kuma kakannina, tare da saka su a cikin buhuna, in kuma yi tafiya don sake binne su a cikin sababbin kaburbura a cikin jeji.”
Labarin Iman ba sabon abu bane. A cikin shekaru biyu da suka gabata, an rusa dubban wuraren kaburbura da dama na Tarihi a Alkahira, cewar cibiyar Hukumar Kula da Ilimi da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO.
Sun hada kuma da wasu a cikin sanannen birnin Matattu.
Gwamnatin Masar na share fage domin samar da sabbin manyan tituna da gadar sama, wanda ta ce zai inganta zirga-zirgar ababen hawa a babban birni mai cike da cunkoso, mai dauke da mutane kimanin miliyan 20.
Hakan kuma zai hada tsakiyar babban birnin kasar da wani sabon titi da ake ginawa mai nisan kilomita 45 zuwa gabashi, aikin kuma da zai lashe biliyoyin daloli.
Aikin da ake yi na a matsayin wani bangare na kokarin sabunta kasar Masar. Tun bayan hawan shugaba Abdul Fattah al-Sisi kan karagar mulki a shekara ta 2014, alkaluman hukumomi sun nuna cewa an gina jimillar tituna masu nisan kilomita 7,000 da kuma wasu gadoji guda 900 a fadin kasar, inda ‘yan kwangilar soja ke gudanar da aikin.
Hukumomin kasar sun dage cewa babu daya daga cikin dimbin abubuwan tarihi da aka yi wa rajista a wannan tsohon yankin na birnin Alkahira da aka lalata, wasu ma tun lokacin yakin Larabawa a karni na bakwai, kuma ana girmama kaburbura masu muhimmanci.
“Ba za mu yi abubuwan da za su lalata kaburburan mutane ba ko kuma na wuraren tarihi. Mun gina gadoiji domin kaucewa hakan,” in ji Shugaba al-Sisi.
“Ba za mu ba da kofa ga wadanda ke son wargaza kokarinmu ba.”
Jami’an shugaban sun ce makabartun da lamarin rushe-rushe ya shafa, yawancinsu sun fito ne daga karni da ya gabata, kuma an biya diyyar lalata su.
Sai dai mutane sun yi ta kokawa kan yadda aka yi hasarar manyan gine-gine masu daraja da kuma wani katafaren ginin tarihi na musamman a wasu makabartu shida na tarihi inda aka dade ana binne fitattun mutanen Masar, galibi an tsara kaburburan cikin yanayi mai kyau wadanda aka zana su da rubutunn Larabci.
Ba a bar Sarakuna da manyan malaman addinin Musulunci da mawaka da masana da kuma jaruman kasa su kwanta kwanciyar hankali ba.
Tare da farin gashinsa da kwararriyar kyamararsa, Dokta Mostafa El-Sadek ya fito domin binciken baraguzan makabartar da aka rusa tare da matasa masu aikin sa kai.
Ya kasance shahararren likitan mata kuma malamin jami’a wanda ya koma barawon kabari.
“Na ji takaicin an cire kaburburan Tarihi na Alkahira. Za mu iya koyan tarihinmu daga makabarta,” in ji Dokta Sadek, wanda ke kokarin ceto duwatsu da sauran kayayyakin tarihi.
“Na yi imanin ya kamata a ceci wadannan taska.”
Ya ba da labarin yadda a cikin wannan wata ya hango wani dutse da aka gina a cikin wata katanga da aka ruguje mai dauke da zane-zane a rubutun Kufic, wani salo na farko na rubutun larabci, a lokacin da yake bincike a makabartar Imam Shafei, daura da titin Sayyida Nafisa.
A tsanake kungiyarsa ta cire dutsen kabarin, inda suka tarar yana da rubutu na wata mata da ake kira Umamah, wanda aka rubuta tun karni na tara.
“Dutsen yana kallona ni ma ina kallonsa. Yana son na raba shi da katangar,” a cewar Dakta Sadek.
Yanzu haka an mika dutsen kabarin ga ma’aikatar yawon bude ido da kayayyakin tarihi da fatan za a baje kolinsa a wani gidan tarihi.
Karkashin daular khalifanci da daular Musulunci a jere, an binne mamatan Alkahira a wannan yanki na birnin, karkashin karamar tudun Mukattam.
A da, kowane iyali mai wadata yana da nasa fili mai katanga tare da makabarta da aka kafa a cikin lambun ganye. Wani lokaci ana kara gine-ginen wajen don daukar dangi masu ziyara kuma in ba haka ba suna gida ga masu kulawa.
Suna kuma tare da masu kashe gobara da masu tona kaburbura da iyalansu, daga baya kuma, dubun-dubatar talakawan Misarawa, da suka zo zama a cikin kaburbura, musamman birnin Matattu, sun zo gidan da ba a saba gani ba, wanda ke fuskantar barazanar ginin.
Wasu mazauna garin sun riga sun amshi tayin gwamnati na kaura zuwa gidajen haya da aka gina a wajen birnin Alkahira.
“Abin takaici, Alkahira za ta yi hasarar al’adun gargajiya masu daraja,” in ji Galila el-Kadi, wata masaniyar gine-ginen da ta yi nazarin birnin Matattu da mazaunanta tun farkon shekarun 1980, da kuma sauran makabartun tarihi.
Ba ta goyi bayan hujjar ma’aikatun gwamnati game da wani sabon tsari da za a yi wa Alkahira ba.
“Ba su san menene ma’anar gado ba, menene ma’anar tarihi,” in ji ta. “Wannan yanayi ne da duk sarakunan da suka shude suka kiyaye a zamanin da da kuma yanzu.”
‘Yan kasuwa masu harkar gine-gine sun dade suna sa ido kan harkar, kuma a tsawon shekaru, Ms Kadi ta yi amfani da bincikenta don shirya taro da ministocin da kuma tsayawa don kokarin kare makabartu.
A wannan karon, hatta shirin hukumar ta Unesco bai yi nasara ba, ko da yake hukumar ta nuna damuwa cewa rugujewar kaburbura da gine-ginen tituna na iya yin babban tasiri ga gine-ginen biranen tarihi na yankin.
An kai gawar Sarauniya Farida matar Sarki Farouk na daya, wanda aka yi wa juyin mulki a shekara ta 1952 zuwa wani masallaci bayan da aka lalata kabarinta.
Har ila yau, cikin kaburburan da aka ruguje, har da na Abdullahi Zuhdi, masanin tarihi na karni na 19 wanda kyawawan ayyukansa suka kawata masallatai biyu mafi girma na Musulunci a Makka da Madina.
An samu wasu nasarori, kamar wani gangami na baya-bayan nan na ceto kabarin babban marubuci kuma masani na Masar na karni na 20, Taha Hussein, bayan da aka saka wa kabarinsa alama da ke nuna cewa za a ruguje shi.
Duk da haka, masu kiyayewa sun nuna cewa ana asarar mutuncin yankin saboda sauran kaburbura da abubuwan tarihi za su zauna su kadai a kasa ko kuma kewaye da sababbin hanyoyi.
“Suna kirkirar tsibirai a kebe, wadanda suka rabu da juna,” in ji Mis Kadi.
Yanzu, ta dukufa wajen samar da bayanai na hotuna da taswirorin yankin.
Mis Kadi ta ce “Wannan mummunan yanayi ne, amma ni da tawagata, da duk mutanen da suka damu da gadon, duk abin da za mu iya yi yanzu shi ne adana abubuwan tunawa da wadannan wuraren,” in ji ta.
“Hakan shi ne hanya kadai ta isar da shi ga al’ummomi masu zuwa.”
Idan muka koma makabartar Sayyida Nafisa, Iman ta kasance cikin dimuwa a yayin da take tono gawawwakin ‘yan uwanta.
Ta bayyana yadda aka aike wa ‘yan uwanta wasika inda aka bukaci su gaggauta daukar mataki bayan sanya su cikin jerin kaburburan da za a rusa.
“Wannan wulakanta matattu ne. Na kasance ina samun kwanciyar hankali idan na ziyarci mahaifiyata da aka binne a nan tare da kakannina,” in ji ta.
“Lokacin da nake cikin bakin ciki ina zuwa nan domn yi mata magana. Wannan kuma shi ne fatan mahaifiyata na karshe na ganin an binne ta a nan tare da mahaifiyarta da kuma mahaifinta.”
Sabon zagayen ginin ya shafi kaburbura 2,600 masu zaman kansu. Ba ya ga damuwa, iyalai da yawa suna korafin cewa diyyar da aka ba su bai taka kara ya karya ba.
“Kakana ya zabi a binne shi kusa da wannan Musulmi kuma ya biya Dala 100,000 a shekarar 2019 don wannan wurin binne mutane a Masallacin Sayyida Nafisa,” in ji wata mata a wani gefen makabarta, wadda ta nemi a sakaya sunanta.
An bai wa danginta sabon wurin binne mutane mai fadin murabba’i 40 wanda ba shi da kima sosai, mai nisan kilomita kusan 55 a wajen Alkahira.
“Wadannan makabartu suna da wadatar gine-gine,” in ji ta.
“Bai kamata gwamnati ta ruguza su ba, kamata ya yi ta mayar da su gidajen tarihi.