Ɗan wasan gaban ƙungiyar Paris Saint-Germain, Ousmane Dembélé, ya zama gwarzon da ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025.
Ɗan wasan gaban na Faransa mai shekara 28, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar PSG a kakar da ta gabata.
- He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
- Jadawalin ‘Yan Wasa 30 Na Farko A Kyautar Ballon D’or Ta Bana
Kulob ɗin ya lashe gasar Ligue 1, Champions League da kuma Coupe de France, abin da ya sa PSG ta zama kulob ɗin Faransa na farko da ya yi irin wannan nasara a Turai.
Dembélé ya yi bajinta sosai, inda ya bada gudunmawar cin ƙwallo da taimakawa wajen zura ƙwallo 43 a wasanni 44 a Ligue 1 da Champions League.
Wannan ne ya taimaka wa PSG ta yi zarra a Turai kuma ta samu nasarar zama ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi a duniya.
An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp