Da sanyin safiyar Laraba ne aka kai hari hedikwatar ‘yansandan jihar Adamawa, lamarin da ya haifar da firgici a Yola, babban birnin jihar.
An kai harin ne a hedikwatar rundunar ‘yansandan da ke tsakiyar garin Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa inda aka kwashe kusan mintuna 30 ana barin wuta.
- Gwamnatin Tarayya Ta Soke Lasisin Ma’adinai 1,633
- Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an dakile harin kuma al’amura sun daidaita.
Harin dai an alakanta shi ne da ramuwar gayya daga jami’an tsaron sojojin Nijeriya, inda kwamishinan ‘yansanda a jihar ya yi Allah wadai da harin.
Cikin wata sanarwar manema labarai, Kwamishinan’yan sandan jihar CP Afolabi Babatola, ya ce fadan da ya faru tsakanin jami’an ‘yansanda da sojoji a Target Junction, cikin karamar hukumar Yola ta arewa, ya haifar da hare-haren da sojojin su ka kai Hedikwatar.
Takardar sanarwar wacce jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Suleiman Yahya Nguroji, ya aikwa manema labarai, ta ce harin da sojojin ya yi sanadin mutuwar Insifekta Jacob Daniel.