Shekaru ashirin bayan mamayar Iraki, har yanzu ana samun ce-ce-ku-ce kan ci gaba da kasancewar makaman kare dangi a kasar wanda kuma ya nuna da hannun Birtaniya a ciki.
An samu sabbin bayanai a wani bincike da BBC ta yi a kan makaman kare dangi bayan shekara 20 da mamayar Iraki da aka yi musamman ma bayan tattaunawa da gwamman mutanen da abin ya shafa.
“Abin mamaki.” Wannan shi ne martanin da wani jami’in rundunar M16 ya yi lokacin da wani abokin aikinsa ya fada masa a 2001 cewa da gaske Amurka take kan yakin Iraki.
Ga Birtaniya, idan aka zo bangaren fadan abubuwa kan Iraki, musamman irin barazanar da makaman kare dangi na kasar ke yi – wani abu ne na yin taka tsan-tsan.
A wani lokaci can baya, an bayyana cewa gwamnatin Birtaniya ta bijiro da zargin mallakar makaman kare dangi da ake yi a Iraki. Sai dai, ministoci a lokacin sun ce an tabbatar musu da cewa babu makaman.
“Yana da muhimmanci a gane cewa irin bayanan sirri da nake samu da su na dogara, kuma ina tunanin cewa da bayanan zan dogara,’’ in ji tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair.
Ya ce a jajiberin ranar da za a kaddamar da mamayar, ya yi tambaya, kuma an ba shi tabbaci daga kwamitin hadaka na tattara bayanan sirri. Ya ki yin suka ga kwamitin kan gazawa da ya yi.
Wasu ministoci sun ce suna da shakku a lokacin.
“Kusan lokuta uku, na aza ayar tambaya kan bayanan sirri da Richard Dearlobe ya bayar,’’ in ji sakataren harkokin waje, Jack Straw. “na matsu kan bayanan. Sai dai, Dearlobe ya tabbatar min cewa za a iya dogara da wadan nan jami’ai.”
Amma, mista Straw ya ce hakan nauyi ne da ya rataya kan ‘yan siyasa, saboda su ne suke daukar mataki na karshe.
Da aka tambaye shi kan gaza samun bayanan sirri a kan Iraki, Sir Richard ya ce “A’a. “Har yanzu ina da yakinin cewa Iraki na da wasu makamai sannan an ma tsallaka da wasu kan iyaka zuwa Syria.
Sai dai wasu basu yarda da hakan ba. “babbar gazawa ce,” in ji Sir Dabid Omand, mai kula da harkokin tsaro da leken asiri na Birtaniya a lokacin.
Ya ce nuna son kai ya sa kwararrun jami’an gwamnati suka saurari bayanan da basu cika ba da ya goyi bayan ra’ayin cewa Saddam Hussein yana da makaman kare dangi, tare da rangwame duk wanda ba shi da shi.
Wasu a cikin jami’an MI6 sun ce su ma sun damu. “A lokacin na ji cewa abin da muke yi bai dace ba,” in ji wani jami’in da ya yi aiki a Iraki, wanda bai taba yin magana ba kuma ya nemi a sakaya sunansa.
“Babu wani sabon labari ko ingantaccen bincike ko sa ido wanda ya nuna cewa Iraki ta sake fara shirye-shiryen mallakar makaman kare dangi da kuma haifar da wata barazana,” in ji tsohon jami’in. “Ina tsammanin daga mahangar gwamnati shi ne kawai abin da za su iya samu.
Jami’an MI6 a Iraki ba su da wani bayani game da makaman kare dangi ko kadan, kuma akwai bukatar son sabbin bayanan sirri daga majiyoyi don karfafa batun, musamman lokacin da aka shirya yin takarda a watan Satumba.
Wani jami’i ya tuno yadda ya nadi wani sakon murya, inda ya ce “babu wata muhimmiyar rawa” ga hukumar leken asirin sama da shawo kan al’ummar Birtaniya kan lamarin don daukar mataki.
Sun ce an yi tambayoyi idan hakan ya dace, kuma an goge sakon.
A ranar 12 ga watan Satumba, Sir Richard ya kai ziyara wani wuri a kan titin Downing bayan samun wata majiya da zai samu sabbin bayanai.
Wannan mutumin ya yi ikirarin cewa ana sake kulla shirye-shiryen, Saddam Husseini kuma ya yi alkawarin bayar da sabbin bayanai nan ba da jimawa ba.
Duk da cewa wannan majiyar ba ta yi cikakken bincike ba, kuma ba a raba bayanansu ga masana ba, an mika cikakkun bayanai ga firaministan.
Sir Richard ya yi watsi da tuhumar da ake yi masa na cewa ya kusanci Downing Street a matsayin “abin ba’a”, Sai dai, ya ce ba zai yi tsokaci ba kan cikakkun bayanai kan karar ko kan majiyoyi ba.
Sai dai a cikin watanni masu zuwa, ba a taba isar da wannan majiya ba, kuma a karshe an yi la’akari da cewa an yi hakan, in ji wasu majiyoyin leken asiri. Sun kuma kalubalanci cewa abubuwa da dama na tabarbarewa.
Sai dai watakila wasu sabbin kafofin na neman bayanai ne don kudi ko kuma don su ga an hambarar da Saddam. A cikin watan Janairu 2003, na hadu da wanda ya sauya sheka daga hukumar leken asirin Saddam a Jordan.
Ya yi ikirarin cewa yana da hannu wajen samar da dakunan gwaje-gwajen tafi-da-gidanka don yin aiki a kan makaman kare dangi, ba tare da ganin masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya ba.
An sanya ikirarin nasa a cikin jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya gabatar ga Majalisar Dinkin Duniya a watan Fabrairun 2003, duk da cewa wasu a cikin gwamnatin Amurka sun riga sun bayar da sanarwar “konawa”, yana mai cewa ba za a amince da bayanan ba.
Wata majiya mai suna “Curbeball”, wadda Amurka da Birtaniya suka dogara da ita, ita ma tana neman yin cikakkun bayanai game da dakunan gwaje-gwajen.
Ana kuma tuna cewa Saddam ya taba mallakar makaman kare dangi. Makonni kadan kafin yakin 2003, na ziyarci kauyen Halabja da ke Arewacin Iraki, na kuma ji mutanen yankin sun bayyana ranar a 1988 da sojojin Saddam suka jefa musu makamai masu guba.
Gaskiyar abin da ya faru da wadan nan makaman ya bayyana ne bayan yakin.
Saddam ya bayar da umarnin lalata yawancin shirinsa na mallakar makaman kare dangi a farkon shekarun 1990 bayan yakin Gulf na farko da fatan samun kudurin lafiya daga masu sa ido kan makamai na Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda daya daga cikin manyan masana kimiyya na Iraki ya shaida min.
Mai yiwuwa shugaban na Iraki ya yi fatan sake fara shirye-shiryen a wani lokaci. Amma ya lalata komai a asirce, domin ya ci gaba da kasancewa da wani abin da zai iya amfani da shi a kan makwabciyarta Iran, wadda suka yi yaki da ita.
Sai dai daga baya lokacin jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka nemi Iraki da su tabbatar da cewa sun lalata komai, sun kasa yin hakan.
Daga baya wani masanin kimiyya na Iraki ya bayyana cewa sun yi watsi da wani wuri mai hadari da hukumomin leken asirin kasashen Yammacin duniya suka ce ba a san inda yake ba, ta hanyar zuba shi a kasa.
Amma sun yi haka a kusa da daya daga cikin fadar Saddam Husseini, kuma suna fargabar cewa sanin wannan gaskiyar zai sa shugaban Iraki ya kashe su.
Sakamakon duk wannan shi ne cewa Iraki ba za ta taba iya tabbatar da cewa ba ta da makamai ba.
A karshen 2002, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun dawo Iraki suna neman makaman kare dangi.
Wasu daga cikin masu sa ido, da suka yi magana da BBC a karon farko, sun tuna da duba wuraren da bayanan sirri daga kasashen Yamma, suka nuna cewa za a iya kafa dakunan gwaje-gwajen wayar hannu.
Abin da kawai suka gano shi ne abin da ake kira da “motar daukakar ice cream” lullube cikin intanet.
Jama’a a lokacin ba su taba sanin cewa yaki na tinkaro su ba, inda majiyoyi suka kasa kai wa, sannan kuma masu binciken sun yi ta jan kunne da kuma nuna damuwa.
“Makomata tana hannunku,” in ji Mista Blair, cikin bacin rai, ga Sir Richard a cikin Janairu 2003, lokacin da matsin lamba ke karuwa don nemo shaidar mallakar makaman kare dangi.
“Abin bacin rai ne a lokacin,” in ji Sir Richard. Ya zargi masu sa ido da rashin kwarewa saboda gaza samun bayanan da ake bukata.
Hans Blid, wanda ya jagoranci tawagar bincike kan duba makaman kare dangi na Majalisar Dinkin Duniya, ya fada wa BBC cewa kafin fara aikin a 2003, yana da yakinin cewa akwai makaman kare dangi, sai dai ya fara sa shakku kan haka bayan fara binciken.
Ya ce yana son karin lokaci domin samun bayanai, amma ba zai samu hakan ba.
Rashin samun “bayanan aikata laifi” bai sa an dakatar da yaki da aka yi a watan Maris din 2003
“Na yi iyakar kokarina wajen ganin ban shiga aikin soja ba,’’ In ji Tony Blair a tattaunawa da BBC.
Shugaba George Bush, cike da fargabar cewa kawayensa za su yi rashin nasara a kuri’ar da majalisa za ta kada a jajiberin fara yakin, ya bayyana a cikin wani hoton bidiyo, inda ya ja da baya kan mamayar, amma ya nuna cewa yana son a dama da shi bayan yakin, sai dai firaministan ya ki aminta da hakan.
Ya kare matakin nasa duka bisa ka’ida dangane da bukatar yin mu’amala da Saddam Hussein, amma kuma saboda bukatar ci gaba da kulla alakar da Birtaniya da Amurka.
“Da hakan zai yi tasiri sosai kan dangantakar,” in ji shi, ya kara da cewa: “Lokacin da nake Firaminista, babu shakka ko dai a karkashin Shugaba Clinton ko Shugaba Bush, kiran wayar waye shugaban Amurkar ya fara daukawa ba.
Yau mun fita daga Turai kuma Joe Biden ya dauki wayar zuwa ga Rishi Sunak? Bani da tabbacin haka.”
Amma ba za a samu wani makamin kare dangi daga baya ba. Wani tsohon jami’in MI6 ya ce, “Duk abin ya wargaje, yayin da yake tunawa da wani nazari na cikin gida da aka yi bayan yakin.
Kuma wannan zai bar babban sakamako mai dorewa ga ‘yan leken asiri da ‘yan siyasa.