Ministan harkokin ‘yansanda, Sanata Ibrahim Gaidam, a ranar Laraba, ya kaddamar da wani sabon ofishin ‘yansanda na zamani a Katampe da ke yankin Mpape a Abuja.
Sabon ofishin ‘yansanda na zamani, wanda Asusun kula da ‘yansanda na Nijeriya (NPTF) ya gina, an mika shi ne ga jami’an rundunar tsaro ta ‘yansanda ta hanyar wakilan Ministan, Dokta Anuma Ogbonnaya Nlia da sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin ‘yansanda.
- A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka
- Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya
Ministan ya bayyana cewa, wannan babban ci gaba ne a kokarin hadin gwiwa na karfafa tsaron cikin gida da kuma kare rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan, tare da bayyana cewa, kammala aikin ofishin da NPTF ya yi, ya shaida karara cewa, gwamnatin tarayya ta himmatu wajen tabbatar da tsaro a karkashin jagorancin ministan harkokin ‘yansanda na inganta al’umma da kuma inganta ayyukan ‘yansanda.
A jawabinsa na maraba, sakataren zartaswa na asusun tallafawa ‘yansandan Nijeriya, Mista Mohammed Sheidu, ya gode wa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa, sadaukar da kai ga bangaren tsaro, kawo sauyi, karfafa cibiyoyi, da goyon bayan da yake bai wa asusun tallafawa ‘yansandan Nijeriya wanda ya yi tasiri sosai, har ya iya gina ofishin ‘yansanda na zamani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp