Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya tare da Sarkin Gombe, Alhaji (Dakta) Abubakar Shehu Abubakar III, gami da dubban al’ummar musulmai ne suka gudanar da Sallar Idi mai raka’a biyu a jihar da ke alamta kammala Azumin watan Ramadana.
Mataimakin babban limamin Gombe, Ustaz Aliyu Hammari, shi ne ya jagoranci Sallar wacce ta hada fuskokin dubban jama’a da jami’an gwamnati, kakakin majalisar jihar da sauransu.
- Sakon Sallah: Gwamna Nasir Ya Yi Kira Da Hadin Kai Don Gina Jihar Kebbi
- Gidauniyar Saraki Ta Kammala Shirin Rabon Abincin Buda-baki
Kazalika, bayan kammala Sallar Idin an gudanar da hawan sallah cikin kasaita da kyale-kyale domin nuna murna da farin ciki da wannan Idin.
A sakonsa na sallah ga al’ummar musulmai, Gwamnan Jihar Gombe, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya al’ummar Musulmin jihar murnar bikin Sallar Idi, yayin da suka bi sahun takwarorinsu na faɗin duniya don alamta ƙarshen azumin watan Ramadan mai alfarma.
A sakonsa na fatan alheri dauke da sanya hannun kakakinsa Malam Ismaila Uba Misilli, Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci Musulmai su kiyaye koyarwa da dabi’un da suka koya a cikin watan na Ramadan, tare da ɗabbaƙasu a cikin rayuwarsu ta yau da kullum don ci gaban al’umma.
Ya jawo hankalin al’ummar jihar wajen yin addu’o’in hadin kai da juriya a tsaka da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi, inda ya tabbatar da cewa matsalolin da ake fama da su a halin yanzu masu wucewa ne, yana mai cewa Nijeriya za ta farfaɗo daga wadannan matsaloli.
Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar Musulmi su ci gaba da dabbaƙa ibadun da suka gudanar a cikin watan mai alfarma tare da dorar da darussan da aka koya a yayin tafsirai don ci gaban addini, da al’umma baki ɗaya, yana mai jaddada cewa Nijeriya tana matukar bukatar mutanen kirki, masu kyawawan halaye don shawo kan munanan ayyukan da wasu ‘yan tsirarun da ba sa nufin kasar da alheri suka haddasa.
Shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa ya kuma jaddada mahimmancin kyawawan dabi’u wajen yakar matsalolin al’umma.
Ya ce, “Wannan lokaci na sallar idi yana nuni da sadaukarwa, kauna da biyayya ga rukunan Musulunci. Don haka ina yi mana wasiyya da mu dabbaƙa darussan da muka koya a wannan wata na Ramadan da nuna kauna ga juna tare da inganta zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu daban-daban”.
“Kamar yadda dukkanmu muka tuna da marassa galihu da talakawa a cikin watan na Ramadan, ina rokonmu mu ci gaba da wadannan dabi’u har bayan Ramadan.”
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na wanzar da zaman lafiya da tsaro, inda ya sha alwashin cewa gwamnatin ba za ta amince da duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyan da ake mora a jihar ba.
Da yake jaddada muhimmancin samar da romon demokradiyya, ya bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnatinsa tana mai da hankali wajen nausa jihar da al’ummarta gaba.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ja hankalin al’ummar jihar su yi amfani da wasu tsare-tsaren da gwamnatin tarayya da ta jihar suka bullo da su don bunkasa tattalin arzikinsu.
Ya kuma bayyana muhimmancin noma wajen bunkasa tattalin arziki da tabbatar da samar da abinci, inda ya bukaci jama’a su yi amfani da damar da za su samu a harkar noma, tare da karkata akalarsu ga sana’o’i masu nagarta, yana mai bayyana kwarin guiwarsa kan al’ummar Jihar ta Gombe.
Ya yi kira ga sarakunan gargajiya, malaman addini, da shugabannin al’umma su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro don ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar, yana mai tabbatar da aniyarsa ta aiwatar da ayyukan raya kasa da tsare-tsaren bunkasa jihar.