Khalid Idris Doya" />

Yadda Aka Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Jihar Gombe

Kananan Hukumomin Jihar Gombe

A jiya Asabar ne aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Gombe wadanda za su shugabanci kananan hukumomin 11 na jihar.
Bayan fafata zaben, shugaban hukumar shiryawa da gudanar da zabe mai zaman kanta ta jihar Gombe (GOSIEC) Alhaji Saidu Shehu Awak, ya sanar da cewa dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar APC da ke mulkin jihar ne suka samu nasara.
Ya kuma ce, sakamakon zaben da jami’an tattara sakamakon zaben gundumomi 114 da ke fadin kananan hukumomin sha daya na jihar suka kawo musu, ya tabbatar da cewa APC ce ta lashe dukkanin kujerun.
A bisa dogaro da dokokin zabe na jihar Gombe, ya ayyana ‘yan takarar APC a matsayin wadanda suka samu nasara a zaben.
Ya kuma bayyana sunayensu kamar haka, karamar hukumar Akko, Abubakar Usman Barambu ne ya samu nasara daga jam’iyyar APC tare da mataimakinsa Mahmud Saleh Tabra; a karamar hukumar Balanga kuwa, Garba Umar (APC) da mataimakinsa Salamu Ezekiel ne suka samu nasara; Billiri, Margret Bitrus shugaba, (APC), Rabaran Pauel Lashobok a matsayin mataimakin shugaban karamar hukumar ta Billiri; a karamar hukumar Dukku kuwa, Jamilu Ahmed Shabewa ne ya samu nasarar zama shugaba inda kuma Umar Manu Malala ya kasance mataimakinsa dukkaninsu daga jam’iyyar APC.
A karamar hukumar Funakaye ma dai haka lamarin yake inda dan takarar APC Ibrahim Adamu Cheldu ya samu nasara a yayin da Muazu A. Yahaya Tongo ya kasance mataimakinsa; karamar hukumar Gombe kuwa, Aliyu Usman Haruna ne ya zama shugaba da kuma Gambo Sulaiman Garko a matsayin mataimakinsa.
Sauran kananan hukumomin sune: Kaltungo wanda Faruk Aliyu Umar ya samu nasarar zama shugaba, a yayin da Solomon Lande ya kasance mataimakinsa; Kwami, Ibrahim Buba, shugaba, Muhammadu Musa Kolo, mataimakin shugaba; Nafada Musa Abubakar Shugaban karamar hukumar da Salisu Shuaibu Dandele a matsayin mataimakinsa kamar yadda hukumar zaben jihar ta sanar.
Awak ya kuma sanar da cewa a karamar hukumar Shongo kuwa Yohanna Nahari ne ya samu nasarar zama shugaban karamar hukumar da mataimakinsa Ambros Alfred; sai kuma karamar hukumar Yalmatu Deba da ta samu sabon shugaba mai suna Shuaibu Umar Galadima da mataimakinsa Garba Usmnan dukkaninsu sun fito ne daga jam’iyar APC.
A lokacin da yake jefa kuri’arsa a mazabar Jekadafari, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya yay aba bisa yadda zaben ya tafi cikin kwanciyar hankali, inda ya tabbatar wa jama’an jihar da cewa za su samu ingancin rayuwa a bisa zaben shugabannin kananan hukumomin.
Ya kuma nuna gamsuwarsa da yadda jama’a suka fito domin kada kuri’arsu.
Shi ma mataimakin gwamnan jihar Dakta Manassah Daniel Jatau yay aba wa jami’an tsaro da jami’an gudanar da zaben a bisa himma da kokarin da suka nuna, yana mai yabon ne bayan da ya jefa kuri’arsa a mazabarsa da ke gundumar Gurma, Degri- Kulani- Sikkam a karamar hukumar Balanga.
Mataimakin gwamnan wanda ya jefa kuri’arsa tare da bin matakan kariya daga Korona ta hanyar sanya kyallen rufe fuska da bada tazara a yayin da yake jefa kuri’ar tasa, ya shaida cewar zaben kananan hukumomi na daga cikin tsarin tabbatar da demokradiyya mai inganci ga jama’a, wanda zai bada damar samar da wakilci na kwarai tun daga tushe wanda talakawa za su amfana kai tsaye.
Dakta Jatau ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da suka suke zaman jiran sakamakon zaben da suka kada, yana mai basu tabbacin cewa abun da suka zaba shi za a basu domin zabe ne mai cike da gaskiya ake gudanarwa.
Dangane da muhimmancin zaman lafiya, ya nemi al’umman jihar da su rungumi dabi’ar zaman lafiya domin kuwa dukkaninsu ‘yan uwa ne da abokai don haka daga husuma bai da amfani wa cigaban jihar, kana duk wanda ya ci a amsheshi hannu biyu domin yin aiki tare a tsira tare.
Dan takarar jam’iyyar PDP a karamar hukumar Gombe Abdullahi Ali Antai, ya shaida cewar ba zabe mai inganci aka yi a jihar ba, yana mai cewa gwamnati mai ci ta yi zane ne ba zabe ba.
Ya sha alwashin daukan matakin da ya dace domin ganin ya kwato hakkinsa, yana mai cewa a matsayinsa na dan takara ko damar gudanar da zaben ma bai samu ba, balle a ce ya ci ko bai ci ba.
“Na zo ban ma ga akwatin zabe ba,” inji shi.

Exit mobile version