Kungiyar Tsoffin Ma’aikata ta Kasa (NUP) a Jihar Adamawa, ta koka kan yadda aka kwashe shekara tara zuwa 14, ba tare da gwamnatin jihar ta biya tsofaffin ma’aikata kudin sallama ba.
Shugaban Kungiyar Tsofaffin Ma’aikata ta jihar, Muhammad Sali ne, ya bayyana haka ga manema labarai a Yola.
- Hajji 2023: Alhazan Jihar Kwara 272 Sun Dawo Gida Nijeriya
- Bidiyon Dala: Gwamnatin Kano Ta Fara Bincike Akan Ganduje
Sali, ya ce shekaru da dama gwamnatin jihar ta gaza biyan tsofaffin ma’aikatan kudaden da su ke bi bashi.
Ya kara da cewa “Shekaru tara gwamnati ta gaza sallamar tsofaffin ma’aikatan jiha, shekara 14 ba ta biya kudaden sallamar tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomin jihar ba, duk da alkawarin da mai girma gwamna ya yi mana,” in ji Sali.
Da yake magana game da kudaden fansho da gwamnatin ke biyan tsofaffin ma’aikatan duk wata, shugaban kungiyar yac e “da ban mamaki har yanzu mafi karancin fansho shi ne 4000, kana da shekaru 60, kana karbar dubu hudu ko kudin magani ba zai maka ba.
“Gwamnatin jihar na biyan dubu 32 mafi karancin albashi, bisa doka dubu 25 za a biya a matsayin mafi karancin fansho a wata, amma mu har yanzu dubu hudu ake ba mu.
“Doka ne, ko an kara albashi ko ba a kara ba, duk shekara biyar ana kara kudin fansho, amma mu an kara albashin ba a kara mana ba, muna rokon mai girma gwamna da ya duba wannan batu.
“Kullum mambobin kungiyarmu mutuwa suke duk da akwai wa’adi, amma rashin samun yadda za a kula da kai da matsalolin rayuwa ke kashe da dama a cikinmu,” in ji Sali.
Kazalika, ya ce kungiyar mai mambobi dubu takwas a jihar, tun 2013 da aka biya su ba a sake biyan tsofaffin ma’aikatan kudaden sallama ba.
Don haka ya jaddada rokonsa ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, da ya yi wani abu domin ceto rayuwar tsofaffin ma’aikatan.
Haka kuma shugaban ya shawarci mambobin kungiyar da su ci gaba da hakuri zuwa lokacin da gwamnan zai share musu hawaye.