A garin Jos, Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya reshen Jihar Filato ta gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna damuwa kan yadda ake kashe mutane a jihar da kuma wasu sassan Arewa ta Tsakiya.
Zanga-zangar ta zo ne bayan hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka a jihar, inda mutane fiye da 100 suka rasa rayukansu.
- Wang Yi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Ministan Harkokin Wajen Sudan Ta Kudu
- Darajar Cinikin Sarin Kaya Da Sayen Kayan Masarufin Sin Ta Karu Da Dala Biliyan 452.5 a Rubu’In Farkon Bana
Maza da mata, matasa da tsofaffi sun fito ɗauke da alluna da ke ɗauke da saƙonni na neman a kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro.
Rabaran Gidion Para, sakataren gamayyar majami’u a jihar, ya ce sun fito ne domin kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi.
Jihar Filato da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya na fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, da kuma matsalolin da suka shafi bambancin addini da ƙabilanci.
A makon da ya gabata, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki sabbin matakai, ciki har da hana kiwon dare da dawo da ‘yan sintirin sa-kai domin taimakawa wajen samar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp