Yayin da ake ci gaba da buga wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, hukumomin Birnin Paris sun yi alkawarin gudanar da gasar da za a dade ana tuna ta yayin da suke karbar bakuncin gasar Olympics ta nakassu ta wannan shekara ta 2024.
Bayan da aka yi gasar wasannin Tokyo a 2021 ba tare da ‘yan kallo ba saboda annobar Korona, sannan ita kuma gasar Rio ta 2016 ta gamu da matsalollin kudi, Birnin Paris ya kasance cikin matsin lamba kan ya gudanar da gasar da za ta kasance daidai da wadda aka yi a birnin Landan a 2012 ko ma gasar ta Paris ta zarta ta.
- ‘Yansanda Sun Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Sojoji Suka Yi Wa DPO Wasagu A Kebbi
- Amfanin Gawasa Ga Lafiyar Dan’adam
Bikin bude gasar da aka yi a satin da ya gabata ya kasance ne a Place de la Concorde, inda aka bayar da kyaututtuka na lambobin zinare 549 ga ‘yan wasan da suka yi bajinta a washegari sannan za a kammala gasar inda za a yi bikin rufewa a filin wasa na Stade de France ranar Lahadi 8a ga wannan watan na Satumba 2024.
An sayar da tikiti kusan miliyan biyu na shiga gasar zuwa yanzu, inda kuma har yanzu akwai 300,000 da ba a saya ba. Bayan irin nasarar da aka samu ta gasar Olympics da aka kammala a Paris hukumomin birnin sun ce wannan soma-tabi ne.
Gasar ta Paris za ta samu ‘yan wasa mata da tawagogin ‘yan wasa da ba a taba samu ba a wata gasa ta nakasassu ta Olympics kuma ana nunawa a tashoshin talabijin a yankuna da dama masu yawan da ba a taba yi ba a baya. Faransa ba ta taba karbar bakuncin wasannin nakasassu na bazara ba, kodayake ta karbi bakuncin wasannin lokacin huturu na 1992 da aka yi a Albertbille.
‘Yan wasa 215 ne za su wakilici yankin Birtaniya a gasar ta nakasassu ta Faris a wasanni 19- wanda hakan an samu ragi kadan a kan ‘yan wasa 227 da suka fafata a gasar Tokyo – inda maza suka kasance 116 da mata 99. Mafi tsufa a tawagar ‘yan wasan ta Birtaniya, ita ce Jeanette Chippington, mai wasan tseren kwale-kwale wadda take da shekara 54.
Wadda ta fara wakiltar Birtaniya a gasar Seoul ta 1988 sannan mafi karancin shekaru kuma ita ce Iona Winnifrith, mai wasan ninkaya, wadda take da shekara 13, sannan kuma akwai mai wasan kwallon tennis ta tebur Bily Twomey mai shekara 14.
Wadda ke kan gaba a cikin wadanda ake sa ran za su ci wa Birtaniya lambar zinariya, ita ce Sarah Storey, wadda wannan za ta kasance gasa ta tara da za ta halarta, inda kuma take sa ran lambobin zinarenta su kai 19 inda take da shekara 46 za kuma ta shiga gasar tseren keke.
Akwai kuma ‘yan wasa Kadeena Cod da Jody Cundy daga cikin wadanda ake sa
ran su yi bajinta, kamar yadda ake sa ran Hannah Cockroft ta ci gaba da mamaye gasar tsere ta mita 100 da kuma mita 800 kuma ta kara yawan lambobin zinariya da ta ci a gasar nakasassu ta Olympic zuwa bakwai.
Sammi Kinghorn shi ma yana daga cikin wadanda ake sa ran za su ci wa Birtaniya zinare, kamar yadda Will Bailey zai yi kokarin za ma zakara a kwallon tennis ta tebur, kamar yadda ya yi a gasar Rio ta 2016.
‘Yar wasan ninkaya Alice Tai ta dawo fage a wannan karon bayan da ta k kasa halattar gasar Tokyo saboda jinya da kuma aka yanke mata kafar dama daga kasan gwiwa a bara, yayin da Jodie Grinham da ke gasar harbin kwari da baka za ta kasance da juna biyu na mako 28 a lokacin da za ta fafata gasar ta Paris.
Wasan tennis na kan keken guragu, Alfie Hewett, wanda sau 30 yana cin babbar gasa, zai yi kokarin cin lambar zinarensa ta gasar nakasassu ta Olympic a karon farko kuma a gasar tseren keke ta nakasassu ta mata Lauren Steadman da Claire Cashmore, wadanda ‘yan makaranta daya ne a da za su sake gogayyar neman cin lambar zinare bayan fafatawa da suka yi a gasar Tokyo ta 2020, wadda Steadman ta yi nasara.
Bayan gasar Olympics din da aka kammala, inda Faransa ta zama ta biyar a jerin wadanda suka fi cin lambobin yabo, kasar za ta so ta ci gaba da wannan kokari a wannan gasar ta nakasassu ma a fannin kwazo da kuma yanayin kawata gasar.
Daga cikin wadanda kasar take sa ran za su ci mata lambobin zinariya akwai Aledis Hankuinkuant, daga cikin wadanda za su rike tutar kasar a lokacin bikin bude gasar Zai yi kokarin ci gaba da rike bajintar da ya yi a gasar ta Tokyo.
Daga cikin zarata na duniya da za su fafata a gasar ta nakasassu ta Paris, akwai Petrucio Ferreira na Brazil wanda zai so ya ci gaba da rike kambinsa na tseren mita 100. Tarihin da ya kafa shi ne na kammala tseren a cikin dakika 10.29. Akwai Markus Rehm, na Jamus wanda zai so ya kara cin kambin gasar tsallen-badake na nakasassu a karo na hudu.
Haka kuma akwai Balentina Petrillo, wacce za ta kasance ta farko da ta fito fili cikin masu sauya jinsi da za ta shiga gasar ta nakasassu ta Olympics, kasancewar an zabe ta, ta wakilci Italiya a gasar mata masu larurar gani.
To amma a 2021, ‘yan wasa mata sama da 30 ne suka sanya hannu a wata takardar korafi da aka aika wa shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Italiya da kuma ma’aikatar tabbatar da raba daidai da wasanni, suna kalubalantar ‘yancin Petrillo na shiga tseren mata.
Kamar dai gasar Olympics da aka kammala a wannan gasar ma ta nakasassu
an hana Rasha da kawarta Belarus shiga gasar saboda yakin Ukraine, to amma akwai wasu ‘yan wasannnin kasashen biyu da aka bari su shiga gasar a matsayin ‘yan ba- ruwanmu, ‘yan wasa ne da aka tabbatar ba sa goyon bayan yakin da Rasha ke yi a Ukraine.
Akwai kuma ‘yan wasa takwas da ke wakiltar tawagar ‘yan wasan Olympic din na nakasassu daga bangaren ‘yan gudun hijira na duniya. Zakia Khudadadi ta fafata a wasan kokawar taekwondo a ranar farko ta gumurzu, ‘yar wasan da aka haifa a Afghanistan, ta wakilci kasarta a gasar Tokyo bayan da aka yi nasarar fitar da ita daga kasar lami lafiya kafin gasar.
A karon farko kasashe uku da a da ba su taba shiga gasar ta Olympics ta nakasassu ba – Eritrea da Kiribati da kuma Kosobo ana damawa da su a wannan karon duk da cewa har yanzu babu kasar da ta lashe sarka ko guda daya.