Dubban mutane ne a ranar Asabar suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tel Aviv da sauran manyan biranen Isra’ila domin tilasta wa Gwamnatin kasar amincewa da yarjejeniyar sako kusan mutane 100 da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta yi garkuwa da su.
“Kada mu sake sadaukar da rayukan sauran wadanda aka yi garkuwa da su,” in ji wani dan uwan wanda aka yi garkuwa da shi kuma aka tsinci garkuwar shi a makon da ya gabata.
- Yadda Ake Buga Wasannin Guje-guje Na Nakasassu A Paris
- Ni Zan Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa A 2027 – Kwankwaso
An harbe Carmel Gat, wata mace da wasu maza hudu, bayan da sojojin Isra’ila suka tsinci gawarwakinsu a ranar Lahadin da ta gabata a wani rami a Gaza.
“Wadanda aka kashen, da tuni suna tare da mu a yau da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya amince da yarjejeniyar sako wadanda aka yi garkuwar da su,” In ji daya daga cikin dangin Gat da aka kashe.