Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake Gashasshen Biredi Wato (Sandwich).
- Ma’aikatar Cinikayya Ta Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Soke Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Sin
- Sin: Tsawaitar Rikicin Ukraine Ba Zai Amfani Kowa Ba
Abubuwan bukata:
Biredi mai yanka-yanka, Bota, Kifin gwangwani, Tattasai da Taruhu, Albasa, Tafarnuwa, jinja, kayan dandano, Mai Cokali biyu:
Yadda za’a hada:
Asamu biredi mai yanka-yanka a shafe shi da bota a ajiye a gefe.
Sai a zuba mai a cikin karamin kaskon miya sai a zuba yankakkiyar albasa a dan soya na minti biyu, sai a zuba jajjagagen su attaruhu din nan a ci gaba da soyawa. A zuba kayan kamshi da kayan dandano, sai a zuba yankakken kabeji. Idan aka tabbatar duk sun soyu sai a dauki kifin gwangwani a tsiyaye man cikinsa sai a faffasa shi a zuba a kai a ci gaba da juyawa har komai ya hade jikinsa.
Akunna injin gasa buredi, sai a dauko wannan buredi mai yanka-yanka wanda aka shafa bota a jiki sai a zuba wannan hadin su kifin nan a jikin bari daya na biredin a tabbatar ko ina ya samu sai dauko wani biredin a rufe da shi.
Sai a dinga jera wannan biredin a cikin injin gashin a rufeta. Idan ya gasu za’ a ji yana kamshi, sai a bude a cire. Ana sha da shayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp