Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai koya muku yadda ake Gurasa Ya Semonbita:
Ana yin gurasa da semobita (wato “semo bread”) kamar yadda ake yin gurasa da fulawa ta al’ada, sai dai a nan Semobita ne za a yi amfani da shi maimakon fulawa.
Abubuwan da ake bukata:
Semovita (kamar kofi 3-4), Yis (Babban Cokali da rabi, idan kuna so ya tashi sosai), Suga (Babban cokali 2), Gishiri ( rabin cokali), Man gyada ko buta (Babban Cokali 2), Ruwa mai dumi (kusan 1–1½ kofi, gwargwadon yadda Semon ya sha)
Yadda za a hada:
Za a samu roba sai a zuba Semobita, yis, Sikari da Gishiri a kwano, a juya su da kyau, sannan a zuba ruwa, a zuba ruwan dumi a hankali a cikin hadin, a na gaurayawa har sai ya koma kulli.
Sai a zuba man gyada ko Bota a ciki, a ci gaba da murzawa har kullun ya yi laushi ba ya manne ba.
Sannan sai a rufe rubar da leda ko zani, a barshi a wuri mai dumi ko a kaishi rana na tsawon awa 1–2, har ya ya tashi.
A shafa man gyada a cikin abin gashi sai a dora a wuta idan ya yi zafi sai a rika zubawa daidai yadda kuke son girmanta, haka har ku gama.
Wannan gurasa da semovita ya kan fi dan nauyi kadan idan aka kwatanta da wanda aka yi da Fulawa na Alkama, amma yana dadi kuma yana daukar lokaci.