Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake hada Boga.
- Amarya Ta Zuba Guba A Abinci Biki A Jigawa
- Yarinyar Da Ake Zargi Da Zuba Wa Mijinta Da Abokansa Guba A Abinci, Ta Amsa Laifinta A Kotu
Abubuwan da za ku tanada:
Biredin Boga, Salad, Tumatur, Ciz na Boga, Albasa, Kokumba, Nama na Boga, Mustad:
Yadda za ku hada:
Da farko idan kuka samu biredin boga sai ku yanka tsakiyarsa ku ajiye shi a gefe, sannan ku gyara tumatur dinku ku yanka shi a kwance wato (Circle) a turance, shima ku ajiye shi a gefe, sannan Kokumba itama ku wanke ta da dan gishiri ko ruwan khal ku yanka ta a kwance, sai albasa itan kuma ku yanka ta a kwance, sannan boga ciz din shima ku yanka shi kashi hudu wato ‘Skuare’ a Turance, sannan salad din ku wanke shi shima a sa mishi gishiri da dan ruwan khal.
Daga nan sai ku dan cire masa wannan dan farin na idan za’a yanka shi amma kar ku yanka, haka za ku barshi ku ajiye a gefe, sannan ku soya naman na boga sannan ku dakko Mustad din sai ku shafa a jikin biredin, sannan salad din ku shimfida a kansa sannan tumatur shima ku jera a kai, sai Kokumba ita ku jera sai albasa itama ku jera sannan ku shifida ciz din shima a sama, sannan ku dakko dayan yankan biredin ku shafa masa mustad din sai ku rufa a kai ku dan sa shi a oven ya dan gasu haka ko kuma a fry pan abun suya. Za ku iya yinsa a karin kumullo ana ci da shayi.
A ci dadi lafiya.