Mafi yawan lokaci, mu ne muke jawo wa kanmu ciwon koda; sakamakon cin abincin da ke da illa ga lafiyarmu. Muna cin duk irin abin da muke so, amma kuma ba ma tunanin abin da zai iya faruwa da lafiyarmu a nan gaba.
Kazalika, yana da matukar muhimmanci a sani cewa; ciwon koda ba na tsofaffi ba ne kadai, hatta yara ‘yan shekara 20 na iya kamuwa da matsalar.
- Za A Samar Da Asibitin Da Zai Yi Amfani Da Hausa Zalla -Sarkin Hausawan Afrika
- Tinubu Ya Sake Nada Farfesa Sheshe Shugaban Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano
Ciwon koda matsala ce da ta shafi kusan kashi 10 cikin 100 na al’ummar duniya baki-daya. Har ila yau, koda na da kananan gabobi masu kama da wake; suna kuma da karfin da suke iya yin muhimman ayyuka a jikin Dan’adam.
Sannnan, su ne ke da alhakin tace abubuwa marasa amfani a jikin mutum tare kuma da sakin sinadaran da ke daidaita hawan jini da ruwa a jiki, sai kuma samar da fitsari da wasu muhimman ayyuka da dama. Akwai hanyoyi daban-daban da wadannan muhimman sassa za su iya lalacewa.
Ciwon siga da hawan jini, su ne abubuwan da suka fi hadari ga ciwon koda. Har ila yau, akwai kuma kiba, shan taba, kwayoyin halitta, jinsi da kuma shekaru su ma na iya kara wannan hadari. Sikari na jini da ba a sarrafa shi ba da kuma hawan jini, na haifar da lalacewar jijiyoyin jini a cikin koda tare da rage karfinsu na yin aiki yadda ya kamata.
A duk lokacin da koda ba ta yin aiki sosai, abubuwa marasa amfani na ginuwa ne a cikin jinni; wadanda ke samuwa daga abinci. Koda na tace sharar ko abubuwa marasa amfani da karin ruwa daga cikin jinin mutum; don haka za a iya cire su daga jikin mutum ta hanyar fitsari. Duk lokacin da koda ta daina aiki, ma;ana ba za ta iya yin aikinta yadda ya kamata ba, wannan yana nufin cewa; koda ta gaza.
Alamomin Ciwon Koda:
-Samun ciwo mai tsanani da kuma karfi a bayanku
-Kumburin kafafuwa da idon sawu da kuma fuska tare da tashin zuciya da amai
-Fitsari da jini- Fitsari ya kan zama ruwan kasa ko ruwan hoda tare da launin ja. Sannan kuma, yana yin kumfa da wari
-Matsalar yawan yin fitsari ko kuma jin zafi yayin fitsarin
Daga taskar Salihannur S. Na’ibi