Ba kowa ne ke iya kula da yadda ake kyankyashe kwan kaji ba, amma ga masu son koya ko sani ga yadda ake yi. Da zarar kaji sun yi kwai, ana so nan take a kwashe su daga wurin da suka yi wannan kwan, musamman ganin cewa; sukan danne kwaikwayen har su fashe.
Wannan dalilin ne ya sa, wasu daga cikin masu yin wannan kiwo na kaji a gidajensu da sauran masu kiwon kaji, suka fi gwammacewa su kyankyashe kajin su da kansu. Don haka, a nan za ka iya sayo ‘yan tsaki haihuwar kwana daya, idan ba ka so ka kyankyashe su da kanka; amma hakan ya fi tsada.
- Ramadan: Wike Ya Raba Wa Musulmai Kayan Abinci A Abuja
- IFAD Da Gwamnatin Tarayya Sun Yi Hadaka Don Bunkasa Aikin Noma A Arewa
Matakin Farko: Kafa Injin yin kyankyasar, wanda wannan ya danganta da yawan kwaikwayen da Injin kyankyasar kajin zai dauka, akasarin wasu Injinan na daukar kwai kamar guda hamsin, sannan kuma idan kyankyasar ta kasuwanci ce; wasu injinan kyankyasar na daukar yawan kwaikwayen da suka kai kimanin kamar dubu daya. Kazalika, za ka bude injin ka zuba kwaikwayen a cikinsa ka rufe kofar injin.
Sannan, ana so ka tabbatar da ka wanke hannayenka kafin ka kwashi kwaikwayen, domin zuba wa a cikin injin kyankyasar don gudun ka da su lalace.
Haka zalika, ana so yanayin injin kyankyasar ya kasance daga yanayin da ya kai 50, 60, ko 75 .
Yanayin Da Ya Fi Dacewa A Yi Kyankyasa: Ana bukatar zuba kwaikwayen a cikin injin, wanda yanayinsa yana bukatar yanayin da kai kamar digiri 99.5 a koda wane lokaci, amma idan ya zarce wannan adadin ko kuma kasa da haka, zai iya lalata ruwan da ke cikin kwan.
Har ila yau, ana so zafin cikin Injin kyankyasar ya kasance ya kai 50 cikin 100, inda ake so a ci gaba da tafiyar da shi a hakan har zuwa wasu kwanaki. Bugu da kari, kafin kwaikwayen su fara kyankyashewa, ana so zafin cikin Injin ya kasance daga kashi 65 zuwa 75 cikin 100.
Mataki Na Biyu: Ana bukatar wanda zai yi kyankyasar kwan kajin, ya tabbatar ya samo kwaikwayen suke da inganci ta yadda hakan zai sa kyankyasar kwaikwayen ya fi yin kyau. Har wa yau, ana so da zarar sun yi kwan, a kwashe su a zuba a cikin Injin kyankyasar, idan kuma babu kwan da za a zuna, za a iya sayowa.
Mataki Na Uku: Kwan na kai wa kwana 21 kafin su kyankashe, ana so zafin Injin ya hau sama sosai, sannan a zuba kwayayen a cikin injin kyankyasar.
Sannan, ana so ka tabatar kana juya kwaikwayan a lokacin da suke cikin injin kyankyasar, akalla kamar sau uku ko biyar ko kuma zuwa bakwai.
Haka zalika, ana so ka ci gaba da juya shi har zuwa kwana 18, daga baya kuma ka kyale su har zuwa tsawon wasu ‘yan kwanaki.
Mataki Na Hudu: Bayan sun kyankyashe a cikin injin, za ka ga kwaikwayen na motsawa, wato a wannan lokacin ne za su fara yin numfashi.