Assalamu alaikum masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan mako cikin shirin mu na Girki Adon Mace. Yau mun kawo muku tsarabar yadda ake lemun Mangwaro da Abarba.
Ga dai abubuwan da za ki tanada: Mangoro, Abarba, Lemun Tsami, Ruwa, Sukari da Kankara.
- Wani Alhaji Ya Sake Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta A Makkah
- Irin Sake Fasalin Kasar Da ‘Yan Nijeriya Ke So
Da farko dai za ki dauko Mangwaronki mai tsoka da abarba da Lemun Tsami, sai ki wanke su tass, ki cire bayan Mangwaronki da Abarba, sai ki yanka su dai dai yadda blender za ta dauka ki kara mata ruwa dan dai dai yadda za ki markada ya yi laushi sosai. Za ki dauko lemun tsaminki sai ki yanka ki matse ruwan lemun tsamin cikin wani kwana sai ki cire kwalon lemun tsaminki zuwa ruwan lemun tsamin cikin markadadden Mangwaronki da Abarba.
Bayan nan za ki zuba sukari daidai yadda kike so sai ki kara ruwa shima dai dai yadda kike so. Kankara ita ce karshen abin da za ki kara a kai shike nan lemun Mangwaroki da abarba ya yi.
Asha lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp