Jihar Edo na daya daga cikin jihohin da suka yi fice wajen noman abarba a kasar nan, inda manomanta a jihar suka ce, noma ne da ake samaun kudi.
Sai dai,nomanta na tattare da kalubalen da ba kowane manomi ne zai iysa yin noman nata ba.
Daya daga cikin manomnata a jihar, Henry Osemwenghogho ya bayyana cewa, suna fuskatar kalubalen rumbuna zamani a jihar na adana ta, inda hakan ke jawo wa manomanta asara bayan sun debe ta.
Sannnan ya kara da cewa sauran kalubalen sun hada da, karancin kudi da rashin hanyoyi masu kyau da za su yi jigilarta zuwa kasuwanni bayan sun debe ta da rashin samun ma’aikata na dindin da za su yi aikinta a gona da sauransu.
A cewar Osemwenghogho a jihar abarba na kara samun kasuwa, musaman ganin cewa, Allah ya albarkanci jihar da kasart noma mai kyau.
Ya kara da cewa, ba wai kawai a kasuwanin jihar Edo ba, tana kuma samun kasuwa a jihar Borno da Kaduna da Abuja da Kano da Legas da Ribers da Enugu da kuma a sauran jihohin da ke kasar nan.
Ya ce, noman abarba bai da wani takamaiman lokacin da ake fara yi, amma akasari ana fara yin noman ne daga watan Fabarairu zuwa na Afirilu.
Osemwenghogho ya kara da cewa, idan manomanta ba su samu damar yinta a sauran kadadarsu ba, za su iya ci gaba da yinta a watan Disamba.
A cewarsa ga wadanda sabbi ne wajen nomanta, da farko ana bukatar su tanadi gona ko kuma su yi hayarta.
Ya kara da cewa ana son su tabbatar da sun yi sharar da kuma kone dukkan wasu hakukuwan da za su iya zame wa amfanin tarnaki.
Ana kuma bukatar su, da su tanadi kudi, don su dauko leburorin da za su yi aikinta a gonar.
Osemwenghogho ya ci gaba da cewa, ana kuma bukatar su da su tabbatar da sun samo ingantancen iri.
Ya kara da cewa, kafin zuwa yanzu ana sayar da tushenta ne daga naira 10,000 zuwa naira 20,000 amma a yanzu farashin ya kai daga naira 50 zuwa naira 100, amma ya danganta da girman da take da shi.
Osemwenghogho ya kuma koka a kan yadda har yanzu ba sa samun wani tallafi daga gwamnati ba, musaman domin su kara bunkasa nomanta a jihar da kuma kasa baki daya.
A cewarsa, koda sun bukaci rance daga hukumomin hada-hadar kudin ba sa samu, inda ya kara da cewa, ya taba neman bukatar rancen amma ba a dauki maganar da wata muhimmaci ba.
Osemwenghogho ya sanar da cewa, ana samun dimin kudaden shiga masu yawa a nomanta, domin ana samun masu sayenta da dama da suke zuwa daga jihar Legas da Abuja da Kaduna da Sakkwato da Ribas da Bayelsa da kuma Kuros Ribas.
Manomin ya bayyana cewa, noman na da sauki sosai domin a koda yaushe, ana samun wadanda suke jiransu saye ta.
“Muna kira ga gwamnatin jihar da ta samar mana da hanyoyi don su dinga sarrafar amfanin da suka noma na abarbar a cikin sauki da kuma samar musu da hanyoyin da za su dinga samun rancen kudin yin nomanta, musamman don su kara fadada fannin na su”.
Ya ce, yana da kadada kimain 30 ta Abarba da suke a ke a yankin Obia ta kudu a jihar ta Edo, inda ya yi nuni da cewa, inda gwamnati za ta samar mana da masana’anta, hakan zai taimaka wajen rage mana asarar da muke yi saboda rashin rumbuna, musamna na zamani na adana ta bayan mun debe ta, hakan zai taimaka mana matuka.
Osemwenghogho ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar masu da hanyoyi don su dinga sarafar amfanin da suka noma na Abarbar a cikin sauki da kuma samar masu da hanyoyin da za su dinga samun rancen kudaden yin nomanta, musamman don su kara fadada fannin na su.
Shi ma wani manomin Osayi A. ya dangata gobara a matsayin babban kalubalen da manoman suke fuskanta, inda ya kara da cewa, akasarin manomanta suna yin asarar kadadar nomansu saboda kalubalen na gobara da kuma sauran kalubalen da fannin ke fuskantar.
Ya kara da cewa, har ila yau ana kuma fusknatar kalubalen canjin yanayi, inda hakan ke janyo fannin babbar illa.
Osayi ya kara da cewa, fannin na noman Abarba, ana samun kudaden shiga masu yawa, amma sai in har idan manomi ya ci gaba da bata kulawar data dace har zuwa lokacin girbe ta, mussaman wajen yawan cire ciyawa a gonar da aka nomata.
Ya ce, idan ka shuka ta a farkon shekara ana son ka ci gaba da nome ciyar da ke cikin gonar domin ta na da saurin fito wa.