A duk lokacin da za ka shuka Albasa a fili, ka tabbata ka shuka Irinta ya kai tsawon kimanin santi mita biyu, zurfin kuma ya kasance ya kai kimain inci daya.
Tsawon Wane Lokaci Albasa Ke Girma Bayan Shuka Ta A Nijeriya?
Mafi akasari, ana girbe albasa ne a watan Nuwamba zuwa Disamba, sannan ta na kuma kai wa tsawon wata uku zuwa hudu kafin ta girma baki-daya.
A Wadanne Jihohi Aka Fi Noman Albasa A Nijeriya?
An fi yin noman Albasa a Jihohin Kano, Kaduna, Jigawa, Sokkwato, Filato, Bauchi da kuma Kebbi, inda a shekarar 2012 kadai, an samar da kimanin yawan tan 240,000 na danyar Albsa, inda kuma aka samar da tan 1,350,000 na busashiyarta.
Har wa yau, a daukacin fadin duniya baki-daya; an amince da Albasa sakamakon irin muhimmancin da ta ked a shi, musamman a wajen hada abincia mai dadi da kuma wasu abubuwa da ta ke da su na da ban.
Akasari daga kashi biyar zuwa takwas na Albasar da ake nomawa, ana yi ne a kakar sanyi, domin ta na jure wa kowane irin yanayi, har ila yau akasari ana shinfida gadon da za a reni Irin Albasa, wanda zai kasance fadin mita daya; fadin kuma ya kasance iya girman Lambu ko kuma gonar da za a shuka Albasar, inda ake bukatar kula da wajen renon har zuwa kwana arba’in kafin a cire shi zuwa wani sabon gurin.
Bayan kammala dukkan gyare-gyare, sai ka sake zuba su a cikin kedojen da za ka shuka ta ko Tukwane kuma kasar noman da ta kasance mara karfi, musamman don Jijiyoyinta su kara habaka da kuma saurin girma.
Albasa ta fi bukatar kasar noman da ke dauke da sinadarai na gargajiya ko kuma sinadaran da ake kira a turance ‘Alkaline Acidic’ da kuma ‘phosphate’, har Ila yau, an fi so a sake mata matsuguni da yamma bayan an yi mata ban ruwa, sannan kuma ana yi mata canjin waje daga tsawon santi mita 5 ko tsawon santi mita 7.5.
Har Ila yau, yana da kyau a rika cire ciyawa; bayan duk sati biyu tare da kuma da yi mata ban ruwa sau biyu a sati, musamman a lokacin kakar sanyi ana bukatar ka yi mata feshi da nau’in maganin feshi mai inganci.
Bugu da kari, ana bukatar manomin Dawa ya dinga zuba mata takin zamani na ‘NPK’ bayan ya canza mata wajen da zai shuka ta, haka nan ita ma Albasa na fara nuna ne daga kwana 84 zuwa kwana 100 bayan an canza mata waje, idan kuma za a yi mata girbi, ana yi ne ta hanyar yin amfani da hannu.