Idan aka ce canji ana nufin canja kudi daga na kasa zuwa kudin wata kasar, kasuwar canji (edchange trade Ko kuma black market) kasuwa CE KO kuma kasuwanci ne wanda ya kunshi canjin kudin wata kasa da na wata kasar.
Kowacce kasa tana farashin kudin ta da kuma kimar su kamar naira,dala,euro da sauransu duka wadannan kudade ne da ake amfani dasu a fadin duniya wadda kuma suna da yanayin darajarsu.
Shi ya sa za Ka ga mutane suna bukatar sanin farashin dala, farashin sepa, farashin riyal da sauran su.
Sai dai a fannin darajar wani kudin yafi wani kudin daraja misali dala tafi naira daraja duka dala daya 700 ne misali za a sayar idan a dala dari za a siyar ka ga 70 d 100 Shi ne jimillan kudin za su kama. To yanayin kimar kudi ya danganta ga yanayin ci gaban kasa da kuma tattalin arzikin ta wata tafi wata kuma akwai abubuwan da Dama ke daga darajar kudi KO kuma su rage su.
Yadda Aikace-aikacen Su Yake
Ita dai masu wannan Sana’ar su Ake Kira da Yan canji.akwai wurare dayawa da Ake iya yi maka canjin kudi kamar banki Wanda su da farashin kasa suke amfani da shi ba na ‘yan kasuwa ba.
Amma su yan canji su yanayin farashin su daban yake dana gwamnati Wanda bankuna suke amfani dashi kuma suma suna saye ne su sayar da kudin su canja dalilin da ke za yi canjin kudi su ne.
1. A turo wa mutum kudi daga wata kasa sai ya zare a kasar sa.
2. Turowar aiki a cikin kasa
3. Kasuwanci
Yadda Ake Farawa
Domin fara wannan sana’ar akwai bukatar jari kamar kowace sana’a.wannan sanaar akwai bukatar jari kamar kowace sana’a, wannan sanaarta na bukatar kudi mai dan yawa saboda saboda idan aka zo yin canij Kazamana Ka na da kudi isasshe.
Samun wuri mai tsaro, kyau da kuma inda mutane za su gane yana da matukar muhimmanci a irin wannan kasuwancin.