Masu karatu assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Barkan mu da kara saduwa a wani makon a filinmu na Dausayin Musulunci.
Har yanzu dai muna nan a kan darasinmu na Yadda Allah Tabaraka wa Ta’ala yake nuna tausayi da kuma girmamawa ga Manzon Allah (SAW).
- Ambaliyar Ruwa Ta Katse Titin Kano Zuwa Maiduguri A Bauchi
- Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
Za mu dan yi waiwaye kadan a game da darasinmu na makon jiya domin ya saje da na wannan makon.
Idan ba a manta ba, mun yi bayanin cewa, Shi Manzon Allah (SAW) sallar dare dole ce a kansa amma sauran al’ummarsa ba dole ba ce. Idan mutum ya so bayan ya yi shafa’i da wuturi sai ya kama barcinsa. Amma kuma ga masu lura, ai kai ba sai an ce maka ka yi ba, domin Manzon Allah (SAW) wanda komai da komai ya samu amma ga shi nan yana yi, ai ya ishe ka ishara. Illa dai kawai kowa ya yi iya karfinsa, kar mutum ya debi mai yawa ya zo ya kasa yi.
To, Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) ba mu saukar maka da wannan Alkur’ani don ka sha wahala ba. Kila an ce ma’anar wadancan haruffan na ‘Daa-hee’ da Allah ya fara rantsewa da su a farkon surar, suna ne daga cikin sunayen Manzon Allah. Kila kuma aka ce ‘Daa-hee’ sunan Allah ne. Kila kuma ma’anar ita ce ya kai cikakken mutum. Kila kuma tana nufin ya kai cikakken Dan Adam, (saboda wasu abubuwan na Alkur’ani Siriniyananci ne irin su ‘zanjabila’). Kila kuma yana daga cikin kuramen baki ne. Idan an tafi a kan Siriniyananci ne aka fassara shi da Larabci, wannan ya sa aka samu fassarar da yawa. Amma kyakkyawar fassarar ‘Daa-hee’ ita ce ‘Allahu A’alamu muraadihi bi zaalik’. Sai dai kuma mun karanto wani Hadisi da Manzon Allah (SAW) ya ce “ina da sunaye guda goma a wurin Ubangijina,” a ciki ya fadi da ‘Yaasiyn’ da ‘Daa-ha’. Wasu Malamai kuma sun ce ma’anar ‘Daa-hee’ haruffa ne yankakku da suka kasance wani sirri a tsakanin Allah Tabaraka wa Ta’ala da Manzon Allah (SAW). A lokacin da Mala’ika Jibrilu (AS) ya saukar da ‘Kaaf-hee-aiyn-saad’, Manzon Allah (SAW) ya ce “na sani (ma’anarsa) – mu cigaba,” ta nan Jibrilu ya san akwai wani sirri a tsakanin Allah da Manzon Allah da bai sani ba.
Kila kuma wani mutum ya tambayi Abdullahi bin Abbas (RA) kan ma’anar ‘Hee-miym-aiynun-siyn-kaaf’ sai ya ce ‘Allahu A’alamu muraadihi bi zaalik’, to akwai Jabir bin Abdullahi a kusa da shi, sai ya kamo wannan mutumin ya ce masa (Abdullahi) ba ya so ya fassara ma ne. Ai ma’anarsa ita ce shi (Abdullahi bin Abbas) da ka tambaya wai Allah zai bashi zurriyya za su zama sarakuna su gina wani gari a tsakanin koramai guda biyu, sunan garin Bagadada, za su yi zalunci dare daya Allah zai halaka su, ita ce ma’anar. Dubi wani sirri na Allah kuma!
Malam Wasidi kuma ya ce abin da Allah yake nufi da ‘Daahee’ shi ne ya tsarkakakke. Harafin farko ‘Damisa-hannu’ farkon sunan Allah ne na ‘Dahiru’ kuma ya ba Manzon Allah shi, sai ‘Hakurin’ kuma farkon sunan Allah ne na ‘Hadi’da shi ma ya ba Manzon Allah (wa innaka la tahdiy ila siradil mustakim, ma’ana wallahi ya Rasulallah kai ma kana shiryarwa izuwa tafarki madaidaici).
Wasu malamai kuma suka ce ma’anar ‘Daa-hee’, harafin farko yana nufin ‘taka’, na biyu yana nufin ‘kasa’, don haka ma’anar ana nufin ya Rasulallah taka wannan kasar, taka kafarka. Saboda Manzon Allah (SAW) idan yana karatu a sallah kafarsa ta gaji sai ya daga daya ta huta, sannan ita ma dayar a daga ta idan ya mayar da waccan har kafafuwansa suka fara tsagewa, shi ne Allah ya ce masa bai saukar da wannan Kur’ani don ya sha wahala ba. Wannan tausayi ne na Allah ga Manzon Allah (SAW).
A karshen rayuwarsa (SAW), Sayyida Aisha (RA) ta ce idan ya tayar da sallar sai ya zauna ya yi ta karatu, sai in ya rage kamar aya hamsin sai ya mike ya yi ta a tsaye sannan ya yi ruku’u (SAW). Don haka, ‘Daa-hee’ a wannan kaulin tana nufin ‘dogaru a kan kasa da kafafuwanka guda biyu, kar ka wahalar da kanka’.
Akwai mahaddata Alkur’ani da suke yin koyi da haka, sukan daga kafa daya su karanta izu goma. Kamar Malam namu (Malam Isah Kofar Mata Kano) lokacin da ya tsufa ba ya iyawa, yakan ce Allahu Akbar, a da yakan tsaya ba sai ya dafa bango ba yakan karanta izu goma a kan kafa daya, sannan ya ajiye dayan ya sake karanta goma. Akwai mazaje Bayin Allah. Amma abin takaici, na ji wani yana karatu yana cewa ‘wa ya ce a karanta Kur’ani duka cikin dare? Ba lada’, inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Mun sangarce ma bare ana fada mana irin haka. Ga wanda Allah ya yi duniya da lahira don shi (SAW) yana yi har sai da Allah ya ji tausayinsa (ya rage masa nauyin hakan). Ba wai hani ba ne a wurin na idan an aikata babu lada ba, na tausayi ne. Kamar dai idan ka ga wani yana wani abu sai ka ce masa ya dan yi a hankali dai, ka ga ba hana shi ka yi ba, ka tausaya masa ne. Ya kamata mu dinga kokari ba sangarcewa ba kawai. Wasu za su kwana kallon talabijin amma ba a ce musu babu kyau ba, sai masu karatun Alkur’ani. Alhali Manzon Allah (SAW) yana karanta aya daya ma har safe kuma yana yi yana kuka. Ya kamata mu dinga yin kokari iya karfinmu.
Wannan ayar da Allah ya ce bai saukar da Kur’ani don Manzon Allah ya sha wahala ba, ta sauka ce saboda abin da Manzon Allah (SAW) ya kasance yana dora ma kansa na rashin bacci da gajiya da kiyamullaili (tsayuwar dare). Malam Wasidi ya ce Alkadiy Abu Abdullahi, Muhammadu bin Abdulrahman ne ya fada mana wannan, da wanin mutum daya ma na daga malaman hadisi. Su kuma sun karbe ta daga Alkadiy Abul-walidi Albajiyyi, shi kuma ya amince daga wurinsa ne, daga asalinsu kuma na cirato ta.
Shi kuma Baji ya ce, Abu Zarri Alhafizu (Masanin Hadisi ba Sahabin Annabi Abu Zarril Gifari ba) ya zantar da mu, shi kuma Abu Muhammadul Hammawiyy ya zantar da shi, shi kuma Ibrahimu dan Khuzaimus Shafiy ya zantar da shi, shi kuma ya ce Abdu dan Humaisi ya zantar da mu, shi kuma ya ce Hashimu dan Kasimu ya zantar da mu, shi kuma ya ce ya karbi hadisin ne daga Abu Ja’afar (Sayyidina Muhammadul Bakir, shi kuma Tabi’i ne, malami wanda Manzon Allah SAW ya ba da bishararsa cewa zai fede ilimi, sannan sika ne wanda malamai suka yarda da hadisinsa), shi kuma ya ce Rabi’i dan Anasin (Tabi’i ne, don ya ga Jabir dan Abdullahi, Sahabin Annabi SAW) ya zantar da shi, sai dai hadisin ‘mursali’ ne, saboda Rabi’i bai fadi wurin Sahabin da ya karba ba, amma kuma karbabbe ne. Rabi’u dan Anas ya ce Manzon Allah ya kasance idan zai yi sallah yana tsayawa a kan kafa daya (a sallar nafila, idan kafar ta huta sai ya sauke ta ya daga dayar) sai Allah ya saukar da ayar ‘Daaha’, ma’ana ‘taka kasa ya Rasulallahi da kafafuwanka duka biyu’, Allah ya ce “ban saukar maka da wannan Kur’ani don ka wahala ba”.
Girmamawar da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a wannan ayar da kyakkyawar mu’amala da tausayi ba su buya ba.
Yana kuma daga cikin ayoyin da za mu kawo a cikin tausayin Allah Ta’ala ga Manzon Allah (SAW)
Rabi’ul Auwal, 14, Minti 18