Ambaliyar ruwan sama ta yi sanadin yankewar titin Kano zuwa Maiduguri a unguwar Malori-Guskuri a karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, saboda hakan, ba zai yi wu a iya wucewa ta hanyar ba, lamarin da ya tilastawa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyin daban.
- Zanga-zanga: Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama Ta Ƙasa Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Matashi A Zariya
- Ina Rokon ‘Yan Nijeriya Su Sake Hakuri, Su Ba Ni Dama – Tinubu
Da yake jawabi a wurin a ranar Alhamis, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jaddada muhimmancin hanyar, wacce ta hada yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo dauki tare da gyara babbar hanyar domin saukaka zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka domin amfanin ‘yan ƙasa baki ɗaya.
Talla