Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a kauyen Natsinta cikin karamar hukumar Jibiya da ke Jihar Katsina ya lalata gidaje kimanin 255, jim kadan bayan dauke ruwan sama.
Lamarin ya faruwa ne sakamakon ruwan sama da aka rika yi ba kaukautawa kwanaki a jere, wanda ya yi sanadiyar korar mutane fiye da dubu daya daga muhallinsu, wanda da yawansu mata ne da kananan yara.
- PCACC Ta Kama Shugabannin Ƙananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahanar Miliyan 660
- Gwamnatin Kano Za Ta Tsara Zamantar Da Magungunan Gargajiya
Sai dai ba a samu labarin rasa rai ba, amma dai mutane da dama sun samu raunuka, wanda yanzu haka suna asibiti suna karbar magani.
Haka kuma mafiyancin gidajen da ruwa ya ruguje gidajen kasa ne wanda a dalilin haka jama’a da dama sun rasa matsugunnisu kuma suna bukatar taimakon gaggawa.
Mai unguwar garin Natsinta, Malam Dayyabu ya nuna fargaba kan faruwar wannan lamari, inda ya ce yanzu abin da ke gabansu shi ne, kokarin samun abin da za su sanya a bakin salati tun da ruwa ya hargitsa duk abubuwan da suke da shi.
“Babu abin da zan ce sai dai mun gode Allah wanda ya kaddara faruwar wannan lamari kuma babu wanda ya isa tambayi dalilin me ya sa, ganin damarsa ce ya yi haka,” in ji mai unguwa.
A cewarsa, kimanin gidaje 250 iftila’i ya shafa, ba a maganar gidajen da ruwa ya kada a yau (Litinin), yanzu haka wasu karin gidaje guda 4 sun kara faduwa sannan kuma wasu guda biyu sun ruguje baki daya.
“Muna kira ga gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Malam Dikko Umar Radda da su taimaka wa al’umma da kayayyakin rufi da katifu da siminti da bulo da kudadai domin su samu inda za su tsugunna su yi barci a yanzu, ” in ji shi.
Sai dai kuma dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Jibiya Honarabule Mustapha Yusuf ya ziyarci kauyen Natsinta domin jajanta masu da ganin irin barnar da ruwan ya yi, inda ya yi alkawari kai kokensu a gaban majalisa domin tattauna yadda gwamnati za ta tallafa wa wadanda wannan bala’i ya shafa.