• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Amurka Ta Yi Kokarin Amfani Da Nukiliya Wajen Tarwatsa Wata

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
Amurka

A shekarun 1950, lokacin da tarayyar soviet ke kokarin ganin ta isa duniyar wata, masana kimiya a Amurka sun yi kokarin kaddamar da wani shiri – na amfani da wata domin firgita tarayyar.

A lokacin da dan saman jannati, Neil Armstrong ya dawo daga duniyar wata a 1969, ya kasance yanayi na tarihin da duniya ke tunawa.

  • Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Kasar Rasha

Sai dai da a ce Armstrong ya dawo da burbushin da zai kasance guba sakamakon makaman nukiliyar da aka rinka harbawa fa?
A lokacin karanta wata mukala a karon farko da ke bayyani kan binciken wata kowa ya yaba da hikimar da aka zuba cikin kwanciyar hankali. Mukalar da kowa ke iya kau da kai. Kuma kusan haka ne ya kasance.

Amma da zarar mutum ya natsu, abubuwan da ke kunshe a bayanai sun sha bamban.
Shirin A119, kamar yada ake kiransa, wani shiri ne na sirri kan yada za a yi amfani da makamin nukiliyyar Hydrogen a tarwatsa wata.

Nukiliyyar Hydrogen na da hadari gaske domin karfinsa ya zarta nukiliyar da aka harba a Hiroshima a 1945, kuma a wannan lokaci shi ne makami na nukiliya da aka kera.
A wannan lokaci tsakanin watan Mayun 1958 zuwa Janairun 1959 babban jami’in sojan sama, Reiffel ya yi ta kai koma kan tabbatuwar shirin.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Duk da cewa binciken nasu na iya amsa wasu tambayoyi kan wata, shirin A119 an tsara shi ne domin wannan aiki.
An tsara bam din ya tarwatse tsakanin wuri mai duhu da haske a jikin wata, domin kowa ya ga karfin hasken fashewar wata, musamman a Kremlin.

Abu guda ke iya gamsarwa ko ba da hujja kan dalilan wannan shiri mai hadari kuma maganar ba ta zarce batun tsaro da zakuwa ba.

A 1950 babu alamar da ke nuna Amurka za ta yi nasara a yaki. Ra’ayoyin ‘yan siyasa da fitattun mutane a Amurka sun nuna cewa Tarayyar Sobiet na kan gaba a bunkasar nukiliya, musamman wajen ci gaba, da adadin makaman da makami mai linzami.
A 1952, Amurka ta fasa makamin nukiliyan hydrogen na farko. Bayan shekara uku Tarayyar Sobiet ta kidimar da Washington bayan gwada nata makamin.

A 1957 sun sake samun ci gaba, da kwace ragamar sararin samaniya bayan kaddamar da Sputnik 1, tauraron dan’Adam na farko da ke zageye duniya.

Hakan bai taimaki Amurka cewa an kaddamar da Sputnik bayan makami mai linzami na Tarayyar Sobiet ba, kuma ba wai ya nuna Amurka ta yi kokari amfani da damar wajen tarwatsa wata ba ne.
An ta nuna bajintar da aka nada a fadin duniya.”

A shekarar 2000, Reiffel ya taba cewa ba don tangadar da aka samu ba, da duniya ta shaida fashewar makamin da aka tura wata.

Wannan wani abin damuwa ne ga muhalli da kuma sojojin Amurka duk da cewa masana kimiya a wancan lokaci na da kwarin-gwiwa.
Shirin A119 na daya daga cikin shirye-shirye da ke zama kamar martani bayan harba Sputnik, a cewar Aled Wellerstein, masanin tarihi da makamin nukilliya.

A ganinsa harba Sputnik, abu ne da ya burge don haka ba sa nadamar nasu gwajin.
Abin da suka yi a karshe, shi ne harba nasu na’urar, da don jinkirtawa, amma fa ba su hakura ba, domin su ci gaba da gwada sa’arsu har zuwa karshen shekarun 1950.
Abin al’ajabi ne, la’akari da tunanin Amurka a wannan lokaci.

Wannan wani yanayi ne da ke nuna abubuwan mamaki da kuma burgewa da suke kokarin gwada sa’arsu.

”Ina ganin a wannan gabar kalmar burgewa da tsoratarwa duk na iya kayatarwa”
Bai tabbatar da tunanin da aka hada wajen bijiro da wannan shiri ba. Amma duk wanda ya kasance cikin tsarin yana da bai wa da zurfi tunani, a cewarsa.

Ba su damu da aikin ba, kuma babu tsoro a tattare da su na abin da zai iya jawo wa milyoyin mutane a duniya.

Masana kimiyya da dama su gwada abubuwa daban-daban, sai dai a wani lokaci suna yarda da cewa lissafin nasu siyasa na da tasiri sosai a ciki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Da Dumi-dumi: Hukumar DSS Ta Yi Wa Ofishin EFCC Kawanya, Ta Hana Jami’an Shiga Ginin

Da Dumi-dumi: Hukumar DSS Ta Yi Wa Ofishin EFCC Kawanya, Ta Hana Jami'an Shiga Ginin

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.