Shaharren Malamin addinin Musuluncin nan kuma shugaban kungiyar masu ilimin taurari na Afirka, Shekih Muhajjadina Sani kano na daya daga cikin fitattun manyan mutanen da kungiyar Arewa Peace Ambassador Forum ta karrama, inda aka nada shi a mastayin jakadan zaman lafiya a wani kasaitaccen taron da aka gudanar a a garin Kano, taron ya kuma yi daidai da bikin ranar zaman lafiya ta duniya wanda majalisar dinkin duniya ta kebe.
Inuwar jakadun zaman lafiya na Arewa”Arewa Peace Ambassador forum “ta gudanarda taron tunawa da ranar zaman lafiya ta Duniya a yammacin ranar Lahadi a birnin Kano.
- Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sashi Na Musamman A NPA Don Inganta Ayyukanta
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano wanda shima ya sani shaidar karramawa ta Ambasadan zaman lafiya, Muhammad Husaini Gumel shi ne ya shugabanci taron da ya sami halartar masana daban-daban suka gabatar da jawabai a kan taken taron da aka yi a kan cin zarafin jinsi.
Ko’odinatan na kasa na inuwar jakadun zaman lafiya na Arewa jakadan Zaman lafiya, Nura Ali Abubakar ya shaida wa ‘yan jarida cewa makasudin gudanar da taron shi ne domin tunawa da ranar zaman lafiya ta Duniya saboda su jakadu ne na zaman lafiya duk abinda yake na inganta zaman lafiya ya kamata suma su taka muhimmiyar rawa akai.
Da ya daga cikin wadanda aka karrama da shaidar jakadan zaman lafiya a yayin taron Sheikh Muhajjanida Sani Kano, Shugaban kungiyar masu ilimin taurari na nahiyar Afirka kuma shugaban gidauniyar jinkai ta Muhajjadina Foundation, Maji dadin masarautar Yakalaje, ya ce gode wa Allah ya yi kuma farin ciki duba da yadda yan’uwa da iyaye da abokan arziki suka halarta domin nuna far in ciki gareshi na zama jakadan zaman lafiya.
Ya kara da cewa wannan kuma ba abin mamaki ba ne domin duo abinda mutum yake na alkhairi al’umma na gani su ji dadi su yaba ba abin mamaki ba ne kaga wanda ka sani da wanda baka sani ba, da wanda baka zata ba su zo dan tayaka murna.
Ya ce wannan zai dada musu kwarin gwiwa cewa abin da suke al’umma na jin dadi suna farin ciki dan haka yana yi wa Allah godiya da suma al’ummar.
Sheikh Muhajjadina ya ce ita kanta kungiyar inuwar jakadun zaman lafiya ganin irin fadi tashi da suka na wayarwa jama’a kai da abubuwa da za su kawo musu zaman lafiya da suke yasa suka karramashi. Domin shi zaman lafiya ba abinda ya fishi suna rokon Allah ya baiwa kasarnan cikakkiyar zaman lafiya ya kara jaddada godiyarsa ga Allah da yadda jama’a suka taya shi murna.
Ambasada Sheik Muhajjadina ya yi kira ga dukkan al’ummar kasarnan a zauna lafiya musamnan matasa su zama masu inganta rayuwarsu da riko da gaskiya da amana da yin hakuri su guji shaye-shayen kwayoyi da zai sa su aikata abinda zai cutar da ci gaban rayuwarsu in suka zama masu tarbiyya za su samu gina lafiyayyiyar zuriya da za ta inganta al’umma.