A daidai lokacin da al’ummar Musulamai a fadin kasar nan ke gudanar da shagulan bikin Babban Sallar Layya, lamarin ta zo wa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali, musamman kukan rashin kudade a hannun jama’a da kuma tsadar kayan bukatu yau da kullum kamar irinsu raguna da shanu da kuma kayayyakin miya.
LEADERSHIP Hausa ta gano cewa an samu hauhawar farashin kayan masarufi ne sakamakon karyewar darajar naira, janye tallafin mai, tashin farashin kudaden sufuri da kuma bukatu da suka karu da daidai sauransu.
A jihohi da dama da wakilinmu ya tuntuba kusan dukka zancen daya ne, domin kuwa da dama wasu ba lallai su iya amfani da kayayyakin miya da suka hada da tumatur, tattasai da tarigu a yayin da suke dafe-dafen abincin sallah ba. Binciken da wakilanmu suka gudanar sun gano cewa albasa ce kadai ke da sauki a wannan lokacin.
Hakan kuma bai rasa nasaba da sauyin yanayin fara shigowar damina da kayan miyan ke ja baya ba tare da fara fitowar sabbi ba da kuma yadda aka samu ninkuwar bukatar amfani da kayan miyan. Duk da hakan dai, wasu da dama sun nuna kwarin guiwarsu na cewa za su yi kokarin lallabawa tare da sayen abun da za su iya wajen dafe-dafen abincin sallah.
Ko da yake wasu al’umma sun yi nuni da cewa shinkafa fara da mai da yaji ne za su dafa a lokacin sallah sakamakon kauce wa tsadar kayan miya.
Da yake zantawa da LEADERSHIP Hausa, wani dan kasuwar kayan miya a Jihar Bauchi mai suna Ibrahim Alhaji Idi, ya shaida cewar, “Kwandon tumatur mafi karanci ana samunsa kan naira dubu 17 a Jihar Bauchi, wanda kuma yake tsaka-tsakiya ana sayar da shi kan dubu 32 kafin ka samu, tumatur mai kyau kwandonsa yana haura dubu 35 a Jihar Bauchi. Yayin da buhun tattasai ya haura naira dubu 52, attarihu kuma dubu 45.”
Ya ce, mutane da dama za su yi amfani da busasshen tumatur ne a wannan sallah, inda mudunsa ke kai wa naira dari 600, yayin da buhun busasshen tumatur din ke kaiwa naira dubu 25.
Kazalika, wani da ke sayar da shanu da raguna mai suna Dauda Mato, ya shaida cewar tsadar dabbobi ba daga su ba ne, yana mai buga misali da cewa hakan yawancin kayan suka zo musu.
“Mutane da dama suna maganar tsadar dabbobi, wasu dabbobin fa jigilarsu ake yi daga wasu wurare a kawo mana, don haka idan kan duba yanayin rayuwar da ake ciki a yanzu dole su yi tsada. Sannan wasu kan cewa ai akwai dabbobin da ake kiwonsu a gida, mu dauka yanzu kana kiwo a gida, ai dole za ka sayo musu abinci da sauransu, to kayan da za ka sayo din sai an yi amfani da ababen hawa wajen jigilarsu, dole farashin jigilar ya tashi sakamakon tsadar mai.
“Abubuwan da suka janyo tsadar dabbobi a bana gaskiya suna da yawa. Yanzu kamar a Bauchi, babban rago da mutum zai yi amfani da shi akwai na dubu dari hudu, akwai na dubu dari da ashirin, sai kuma kananan da za a su gangaro kasa da haka, amma dan dama-dama wadanda kuma mafi yawanci irinsu aka fi saya su ne ‘yan dubu 80 zuwa 70.
“Sai dai a zahirin gaskiya mutane sun fi sayen shanu a maimakon raguna. Kuma da yiyuwar ma za a yi bandaron dabbobi a bana. Ga shanu da ragu jama’a kuma na kukan babu kudi da tsadar kayayyaki,” in ji Mato.
Wakilinmu na Jihar Zamfara, Hussaini Yero ya shaida mana cewar, sakamakon yanayin da jihar take ciki a halin yanzu, su kam bana ba maganar shanu suke yi ba, inda kuma ya nuna cewa raguna kam ba su tabuwa.
“Ka san babu Fulanin da ke kawo shanu, raguna ne kawai. Yanzu karamar rago mai dama-dama zai haura dubu 70, in kuma kana neman mai dan girma sai ka saya dubu 100.”
Dangane da tsadar kayyakin miya kuwa, ya nuna cewa karamar kwando tumatu ya haura dubu 20, yayin da tattasai kuma ya haura dubu 35 tare da attarihu babban buhu da ake sayansa dubu 50.
A gefen walwala kuwa, ya nuna cewa kusan mafi rinjaye na ma’aikatan jihan sun yi amfani da albashin da sabon gwamnan Jihar Daudau Lawal ya biyasu ne wajen biyan basukan da ke kansu. Ya nuna cewa watanni uku suka gabata ba a biya ma’aikatan albashi ba, don haka ne basuka suka musu yawa.
“Da dama da suka samu albashi da sabuwar gwamnati ta musu na watanni biyu, sun maida hankali ne wajen biyan basukan da suka ci. Mu dai a Zamfara za mu iya cewa alhamdullahi Sallah dai ta zo haka kuma sai godiya.”
Muhammad Gambo Aminu, ma’aikacin gwamnati ne a Jihar Kano, ya shaida mana cewar, “Gaskiya mun samu albashi a kan lokaci, to amma ba zan kwashe kudin wajen sayan dabbobi da su ba. Ni dai gani nan ne, in hali ta bayar zan yi layya, in babu dama kuma za a mu hakura. Domin abubuwan sun yi tsada sosai. Ina daukan albashin da bai kai dubu dari da talatin ba, zan je na sayi ragon dubu dari ne? da me za mu ci abinci da sauran lokutan?”
Har ila yau, Iliya Abubakar daga Jihar Gombe ya shaida mana cewar, tsadar kayan bukatu a bana sun janyo wa jama’a damuwowi da dama wanda ba lallai jama’a da dama su iya yin layya ba.
Ya bayyana cewa duk da yanayin da suke ciki babu takuri sosai, amma ba lallai mutane da dama su iya yin layya ba sakamakon matsatsi da kuma tsadar kayan bukatu da ake fuskanta.
Idris Umar a Zariya, ya labarto mana cewa, ana sayar da kwandon tumatur naira dubu 35, yayin da kuma ake sayar da busashshe tiya naira dubu 8,500, farashin karamin buhun attarihu naira dubu 30 ake samu a Zariya kuma a samu kwandon albasa a naira 1,000 wanda shi ne mafi sauki a kayan miyan bana.
A bangaren dabbobi kuwa, ya ce ana samun raguna ne daga kan dubu dari biyu zuwa kasa, amma zancen kamar ko’ina mai dama-dama dai na haura dubu 80.
Hajiya Fatima A. Adam, wata uwace, ta misalta halin da ake ciki a matsayin yanayin da aka samu kai sakamakon sauye-sauye.
“Kusan komai ne fa ya canza ya tashi, rayuwar ce yanzu sai godiyan Allah. Amma muna fatan sauye-sauyen da ake samu za su saukaka wa jama’a wahalalhalun rayuwa a nan gaba.
“Muna kuma kyautata zagon tsare-tsaren da gwamnatoci suke kawowa za a moresu nan gaba. Don haka fatanmu a nan shi ne, a yi bukukuwan sallah lafiya, jama’a kuma su daure domin nan gaba kadan za a iya samu sauki,” ta shaida.
A bisa wadannan batutuwan, LEADERSHIP Hausa ta zanta da Farfesa Ahmad Sanda, shehin malami kuma masani a bangaren tattalin arziki (Economy) da ke koyarwa a jami’ar Usmanu Danfodio a Jihar Sakkwato a tsangayar koyar da nazarin tattalin arziki, inda ya yi fashin baki kan lamarin da ake ciki tare da cewa, karyewar darajar naira, cire tallafin mai da ninkuwar bukatun a lokutan sallah ne suka janyo tsadar kayan amfani.
Ya ce: “Ka san kasashen makwabta su na kawo kayansu Nijeriya a manyan kasuwanni.
Ka ga faduwar darajar naira ya taimaka wajen karuwar tsadar kaya, domin duk abun da za a shigo da shi daga waje, tun da naira ta fadi ka ga zai taho da karin kudinsa kenan.
“Baya ga wannan, ga batun janye tallafin mai da aka yi wanda ya haifar da karuwar hauhawar farashin kayayyaki saboda tsadar sufuri, hakan ya janyo karuwar kudaden sufuri, daga wani wuri zuwa wani waje. Ka ga idan mai ya kara tsada, komai zai kara tsada don haka za a samu tashin kayayyaki.
“Sannan kuma kamar su tumatur da tattasai daman tun can fil’azal idan irin wannan lokacin ya zo kowace shekara ana samun karancinsu, kusan kayan noman rani ne mafi yawa, don haka idan irin wannan lokacin ya zo ana samun karancinsu wannan kusan kowace shekara ne.
Ka ga an samu hauhawar farashin kayayyaki wanda faduwar darajar naira ya haifar, sannan kuma ga karancin wadannan kayayyaki su ma sun taimaka wajen tashin farashinsu.”
Farfesan ya kara da cewa, “Da ma ka san ita sallah an saba da bukatu suna karuwa sosai kuma mutane da dama na tafiya daga nan zuwa can domin gudanar da shagulgula.
“Abin yah ade ga sallah, ga karin farashin sufuri saboda janye tallafin mai da aka yi ga kuma faduwar darajar naira saboda sabbin tsare-tsaren gudanar da harkokin kudi na babban bankin kasa, to ka ga dukka wadannan abubuwan sun taimaka wajen kawo wannan hauhuwar kayayyaki.”
Masanin ya nuna kwarin guiwar cewa nan gaba abubuwa za su saukaka wa jama’a. Ya yi fatan gudanar da bubuwan sallah lafiya a fadin kasar nan tare da addu’ar Allah ya kawo bunkasar ci gaba mai daurewa a Nijeriya.