• English
  • Business News
Friday, July 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 weeks ago
in Manyan Labarai
0
nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram
  • An Yi Asarar Naira Tiriliyan 25 A Cikin Shekara 25 – Abdulrasheed Bawa
  • Za A Iya Kawo Karshen Lamarin – Masana

Tsohon shugaban Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya fallasa wasu manyan ayyuka na zamba da wasu mutane, jami’an gwamnati, ma’aikatu, da hukumomi (MDAs), da kamfanoni masu zaman kansu suka tafka, a zamanin da gwamnatin tarayya ta rika bayar da tallafi.

A cewarsa, tsawon shekaru 25 masu aikata laifin sun yi amfani da hanyoyin da suka bi wajen damfarar kasar biliyoyin Naira ta hanyar yin takardun jabu, karya wajen bin hanyoyin biyan kudi da wawure dukiyar kasa.

A lokacin da shugaban kasa mai ci Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, Nijeriya ta kashe Naira tiriliyan 16.5 wajen biyan tallafin, wanda akasarinsu duk aka sace.

Tinubu dai a jawabinsa na kaddamarwa ya bayyana cewa ” tallafin man fetur ya kare”.

Bawa ya ce an yi wannan satar ne a karkashin gwamnatoci hudu tsakanin 1999 zuwa 2023.

Labarai Masu Nasaba

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023).

Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta.

Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin Obasanjo ta zo na uku da Naira biliyan 812 yayin da ‘Yar’aduwa ke biye da Naira biliyan 794.

Obasanjo da Buhari sun shafe shekaru takwas suna mulki yayin da Jonathan ya yi mulki na tsawon shekaru shida, tun da farko ya kammala shekaru biyu da gwamnatin Yar’adua ta bari, a matsayin mataimakin marigayin, inda ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2011.

A cikin littafin mai shafuka 317, Bawa ya ce kudaden tallafin, wadanda galibi na yaudara ne, ana samun su ne ta hanyar rashin isassun tsare-tsare, raunin tsarin aiwatar da doka, da kuma rashin gaskiya a cikin dukkan tsarin.

Bawa ya ce wadannan kura-kurai sun karfafa karuwar kudaden tallafin daga Naira biliyan 123 a shekarar 2006 zuwa Naira biliyan 886 a shekarar 2014 da kuma mummunan adadi na Naira tiriliyan 11 a shekarar 2023.

Tsohon shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa za’a iya bayyana badakalar tallafin man fetur ta Nijeriya ta hanyar amfani da triangle na zamba na “Tsarin (Needs), Opportunity and Rationalisation.”

Ya ce, “Matsi shi ne abin da zai sa mutum ya yi zamba, samun dama kuma ita ce ke bayar da yanayin da mutum zai aikata zambar.

 

Yadda Aka Aiwatar Da Badakalar

Bawa ya gano hauhawar farashin shigo da kayayyaki, da sauya lokacin daftarin kaya, rashin bayyana dawo da kayan da aka shigo da su ta sama da kasa, da jirgin ruwa mai yawo, shigo da kaya guda daya, tare da biyan tallafi a kansa sau biyu, na daga cikin hanyoyin da aka tafka badakalar tallafin man fetur.

A cewarsa, kamfanonin sayar da man sun yi amfani da yawan shigo da kayayyaki don kara yawan kudaden tallafi daga karshen shekarun 2010.

Ya ce binciken da aka gudanar ya sa hukumar EFCC ta gano haramtattun kudaden da suka haura Naira biliyan 30.

Bawa ya ci gaba da cewa, “A lokuta da dama, an samu jami’an gwamnati da saninsu ko kuma ba da saninsu ba, ta hanyar buga tambari da sanya hannu a cikin takardun jabun, wasu jami’an sun ce sun sanya hannu a kan takardun a lokacin da suke bakin aiki, duk da cewa suna sane da cewa lamarin ba haka yake ba, akwai wadanda suka sanya hannu kan takardun bogi, ba tare da sanin cewa an kirkiresu ba ne.

Ya ba da misali da yadda wani kamfani ya shigo da lita miliyan biyar kasa da mai fiye da lita miliyan 12. An biya kamfanin tallafin Naira miliyan 700, wanda bai cancanta ba.”

Wannan a cewarsa lamari ya ci gaba da haifar da tambayoyi masu mahimmanci game da hanyoyin damfara, gazawar sa ido na hukumomi, da kuma yadda EFCC ta gano wadannan haramtattun ayyuka.

 

Hanyar Kawo Karshen Lamarin

Dangane da kokarin hukumar na duba matsalar, Bawa ya ba da tarihin bincike, kamawa, tuhume-tuhume, yanke hukunci da kwato haramtattun dukiyoyi da hukumar ta yi.

Ya ce duk da cewa ba a samu wasu laifuka ba a shekarar 2006 da 2007, hukumar ta kwato Naira biliyan 11.5 a shekarar 2008, Naira biliyan 4.88 a shekarar 2009, da kuma Naira biliyan 10.3 a shekarar 2010.

Tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana wata badakala da aka yi a 2011 ta tallafin man fetur, “a lokacin ne muka gano wasu haramtattum ayyukan da suka kai Naira biliyan 41.7.

“A dunkule, ayyukan damfara sun kai kusan Naira biliyan 68, wanda kusan kashi 80 cikin 100 an kwato su,” in ji shi.

Bawa ya kara da cewa, a cikin shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya, Nijeriya ta kashe Naira tiriliyan 16.5 wajen bayar da tallafi, inda ya kara da cewa abin da ke daure kai ga daukacin al’amura shi ne yadda aka kashe kaso daga cikin kudaden wajen yin ikirarin karya da satar dukiyar kasa.

 

Hanyar Samun Ci Gaba

Bawa ya yi nuni da cewa, shi tallafin a kansa ba wani sharri ba ne; amma duk da haka, aiwatar da aikinta na yaudara ya sa gwamnati ta ki amincewa da dimbin albarkatun da aka tanada domin samar da ababen more rayuwa, inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, wadanda ke amfanar da marasa galihu a Nijeriya.

Don haka ya yi kira da a samar da ingantaccen tsarin bayar da tallafi.

Ya ce, “Kiyaye tsarin tallafin da aka sarrafa da kyau zai iya ba da agajin da ake bukata ga masu rauni ta hanyar tabbatar da cewa an dakatar da tsadar rayuwa, sannan gwamnatin ta tsaya tsayin daka wajen samar da wani abin dogaro ga matsalolin tattalin arziki.

“Wannan yana jaddada muhimmancin samar da ingantattun hanyoyin sa ido da daidaita yadda ake raba tallafin don hana cin zarafi da tabbatar da sun cika manufarsu.”

Bawa ya kuma yi kira da a ji tsoron Allah da gaske da kuma samar da ingantaccen tsarin adalci.

Bawa ya ce, “Tsarin ba wai kawai kayan ya ke ba wa kariya da kuma dakile laifuka ba, har ma ya mallakar karfin bincike da kuma hukunta laifukan da suka dace, yana da matukar muhimmanci, irin wannan tsarin na samar da amana da amincewa a tsakanin ‘yan kasa, tare da karfafa hadin gwiwar jama’a da kuma tabbatar da doka da oda.”

Tsohon shugaban na EFCC ya bukaci ‘yan Nijeriya da na kasashen waje da su canja halayensu, su bi ka’idojin da’a, su sanya al’ummar kasa a zuciyarsu sama da kansu.

Bugu da kari, ya yi kira da a samar da isassun kudade tare da tura fasahar kere-kere a cibiyoyin gwamnati domin dakile cin hanci da rashawa.

“Su koma al’adar yin abin da ya dace, ba tare da la’akari da yanayin ba, hakan na iya haifar da sauye-sauye masu dorewa a cikin al’amuran al’umma,” in ji shi.

LEADERSHIP Sunday ta ruwaito cewa an samu wasu ‘yan Nijeriya da dama da laifin zamba a cikin tallafin man fetur, na baya-bayan nan shi ne Mamman Ali, dan Ahmadu Ali, tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya

Next Post

Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka

Related

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace
Manyan Labarai

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

5 hours ago
‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

6 hours ago
Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
Manyan Labarai

Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram

24 hours ago
Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota
Manyan Labarai

Ɗan Wasan Liverpool, Diogo Jota, Ya Mutu A Hatsarin Mota

1 day ago
Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami
Manyan Labarai

Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami

1 day ago
Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
Manyan Labarai

Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu

1 day ago
Next Post
Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka

Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana'antu 10 Na Afirka

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato

July 4, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

July 4, 2025
Ba A Taɓa Nuno Bidiyon Shugaban Jam’iyyarmu Ta ADC Yana Cusa Dala A Aljihu Ba —Dalung

Ba A Taɓa Nuno Bidiyon Shugaban Jam’iyyarmu Ta ADC Yana Cusa Dala A Aljihu Ba —Dalung

July 4, 2025
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

July 4, 2025
Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci

Ayyukan ‘Yan Ta’adda Na Barazana Ga Shirin Gwamnati Na Wadata Kasa Da Abinci

July 4, 2025
Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

July 4, 2025
‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi

July 4, 2025
Yawan Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Da Ganga 177,000 A Janairu

Kungiyar MEMAN Ta Yi Maraba Da Shirin Dangote Na Rabar Da Man Fetur

July 4, 2025
NPA Ta Bukaci Samar Da Tsare-tsare Kan Baraguzan Jiragen Ruwa A Cikin Teku

NPA Ta Bukaci Samar Da Tsare-tsare Kan Baraguzan Jiragen Ruwa A Cikin Teku

July 4, 2025
Sin Na Kara Rungumar Nau’o’in Makamashi Marasa Gurbata Muhalli

Sin Na Kara Rungumar Nau’o’in Makamashi Marasa Gurbata Muhalli

July 3, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.