Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sha kashi a hannun Newcastle United da ci 4-1 a wasa na biyu na gasar Uefa Champions League ta bana.
PSG wadda ta ke a rukunin F tare da Newcastle, Borrusia Dortmund da AC Milan ta koma matsayi na biyu.
- Tattalin Arzikin Afirka Zai Durkushe – Bankin Duniya
- Me Ya Sa Aka Kasa Shawo Kan Matsalar Hare-haren Bindiga A Kasar Amurka?
Ana ganin cewar wannan rukuni na F shi ne rukunin da ya fi kowane rukuni zafi a gasar ta bana.
Shekaru uku da suka gabata kungiyar kwallon kafa ta PSG ta samu damar buga wasan karshe na gasar Uefa Champions League kafin Bayern Munich ta doke ta da ci 1-0.
Manyan ‘yan wasa kamar Messi, Neymar da Sergio Ramos duk sun bar kungiyar a bana abin da wasu ke ganin shi ne silar kasa tabuka abin a zo a gani.
Amma hasashe ya nuna cewar ba lallai ba ne kungiyar ta Faransa ta iya zuwa mataki na gaba ba ganin cewar akwai kungiyoyi irin su AC Milan da Newcastle da ke gabanta.