• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Bullar Cutar Gansakuka Ta Sa Manoman Citta Tafka Mummunar Asara A Kaduna

by Abubakar Abba
2 years ago
Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna, na fuskantar barazanar tafka asarar naira biliyan 10, sakamakon bullar cutar Gansakuka da ke yi wa Citta illa, wanda hakan ya sa wasu daga cikin Manoman cittar fadin a jihar, suka bukaci a kawo musu daukin gaggawa.

Sakamakon bullar  cutar  a Kudancin Kaduna,  Kungiyar Manoma Cittar ta Kasa (NGAN), tare da hadin guiwar wasu wadanda ba Manoma ba, sun tallafa wa Manoman Citta 18; kowannensu da naira 50,000, domin rage musu radadin annobar cutar.

  • Hajjin Badi: Dalilin Kara Kudin Kujera Zuwa Naira Miliyan 4.5 – NAHCON
  • Share Fagen Gasar Kofin Duniya; Messi Ya Zura Kwallo A Ragar Ecuador

Kazalika, kungiyar Manoman Cittar ta bayyana cewa, kakar noman Citta ta shekarar 2023 a Kudancin Kaduna, ta samu babbar koma baya, sakamakon bullar wannan cuta, inda ta koka kwarai da gaske a kan cewa, hakan ya yi matukar jawo asarar sama da naira biliyan 10, da ya kamata a shigar a wani fannin da ya shafi tattalin arzkin jihar.

A taron manema labarai na Karamar Hukumar  Kachia da ke Jihar ta Kaduna, Shugbana Kungiyar na kasa N.B Daudu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma ta Jihar Kaduna, da su samar da sinadaran karya cutar ta Gansakuka.

Bugu da kari, da yake yin tsokaci a kan noman Cittar, Shugaban ya sanar da cewa, sakamakon rashin samun inda ake sarrafa Cittar, yasa ba ta iya shiga gasa a kasuwar duniya.

LABARAI MASU NASABA

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

Daudu ya sanar da cewa, akwai bukatar a samar da inda za a rika sarrafa ta, domin kai wa wani mataki a duniya.

Ya kara da cewa, rashin sarrafa ta da kuma yadda ake hada ta, ya janyo ana barin Nijeriya a baya wajen nomanta da kuma fitar da ita zuwa kasashen ketare .

Su ma a nasu jawaban, Shugaban Karamar Hukumar Kachia Aaron Bako da kuma Daraktar Ma’aikatar aikin noma da kula da gandun daji, Kueen Saidu sun sanar da cewa, noman Citta shi ne sana’ar da al’ummar yankin suka fi mayar da hankali a kai, domin samar wa kansu da kudaden shiga.

A cewar tasu, fannin noman Citta a yankin na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin wannan kasa, shi yasa muke kira ga matakan gwamantin kasar nan, da su taimaka wa Manoman Cittar a yankunan da wannan cuta ta yi wa gonakansu illa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Noma Da Kiwo

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
Noma Da Kiwo

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Next Post
Wata Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kashe Fiye Da Mutum 820 A Morocco

Wata Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kashe Fiye Da Mutum 820 A Morocco

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.