Dangin amarya da ango sun bai wa hammata iska a wajen daurin auren ‘ya’yansu a kan sadaki a yankin Haryana a Indiya.
Daga baya an fasa auren, yayin da ango ya koma gida ba tare da amaryarsa ba, su kuwa dangin kowane ya nufi asibiti da raunuka sakamakon dambe da suka sha.
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Sama Da Mutum 50 A Kongo
- Kasar Sin Ta Shigar Da Kara A WTO Kan Matakin Amurka Na Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje
Majiyar Dainik Bhaskar ta rawaito cewar dangin ango sun bukaci sadaki a lokacin da ake tsaka da biki, wanda dangin amarya suka ce ba su da shi hakan kuwa ya harzuka su.
Amaryar da mahaifinta Vijay Kumar, sun zargi iyayen ango da yanka musu sadaki mai tsada har kudi lak 5.
Har ila yau, sun zarge su da fara kai wa iyalan amarya hari inda suka yi wa kawunta Deepak and Dharmendra rauni.
Sai dai mahaifin angon, Mani Ram, ya musanta zargin inda ya ce hatsaniya ta kaure ne sakamakon zuwan iyayen amarya a makare wajen bikin.
Mani Ram, ya shaida cewar mutane da yawa daga tsaginsa sun sami rauni, kuma yanzu haka suna asibitin Hisar inda ake kula da su.
Wani jami’in dan sanda a yankin, ya ce tuni aka shiga da koke kan lamari, kuma suna gudanar da bincike.