Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya bi sahun dubban al’ummar musulmi a babban filin idi na tsakiyar birnin Yola domin gudanar da sallah.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Barista Auwal Tukur, manyan jami’an gwamnati, da shugabannin masana’antu suma sun halarci sallar.
- Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
- An Kashe Mutum 2, An Raunata 3 A Wani Sabon Hari A Filato
Bayan gudanar da sallar, Khadi Ahmadu Bobboi, babban limamin masallacin Modibbo Adamawa, ya gabatar da wa’azi mai taken tarihi da muhimmancin Idin Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi.
Bobboi ya yi magana game da nau’o’in dabbobin da ake yankawa, ya kuma jaddada muhimmancin yanka dabbobi masu lafiya bisa hadisan Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
A cikin sakonsa na Sallah, Wazirin AdamWa Alhaji Atiku Abubakar ya taya al’ummar musulmi barka da Sallah tare da yi wa alhazan Adamawa da ke Saudiyya fatan gudanar da aikin Hajjin bana karbabbiya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su ji tsoron Allah su koyi zama lafiya da ‘yan uwansu, inda ya bukaci gwamnatoci da shugabannin al’umma da su koya wa talakawansu dangantaka mai kyau da jituwa.
Ya nuna damuwarsa kan rashin fahimtar juna da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin makiyaya da manoma a jihar, inda ya bukace su da su mutunta juna domin samun zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin da ya dace a kan masu aikata laifin.
Ya gode wa Gwamna Umaru Fintiri bisa cika alkawuran da ya dauka na samar da ci gaba ga al’ummar jihar, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba shi basira don ci gaba da ayyukan alheri a wa’adinsa na biyu.