Wani binciken jaridar Premium Times na musamman ya tona asirin irin yadda tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya janye hannun jihar daga kamfanin Dala Inland Dry Port Limited, inda ya mayar da hannun jarin jihar ga ƴaƴansa, kafin ya ba da kwangilar aikin gina kayayyakin more rayuwa a tashar akan biliyoyin Naira.
Binciken da aka yi ya nuna cewa, a shekarar 2020, Gwamna Ganduje ya yi wata yarjejeniya a asirce wadda ya musanya hannun jarin Kano na kashi 20 cikin 100 a kamfanin Dala Inland Dry Port, ya kuma sanya ƴaƴansa uku – Abdulaziz, Umar, da Muhammad Abdullahi Umar – a matsayin masu hannun jari kuma daraktocin kamfanin.
- Gwamna Yusuf Ya Samu Kuɗaɗe A Cikin Wata 6 Fiye Da Yadda Na Samu A Cikin Shekaru 8 – Ganduje
- APC: Ko Sadaukarwar Ganduje Za Ta Dakile Barazanar Jam’iyyun Adawa A Zaben 2027?
Yadda Aka Fara Maganar Hannun Jarin
A shekarar 2006, lokacin mulkin Gwamna Ibrahim Shekarau, Jihar Kano ta sayi hannun jari na kashi 20% a kamfanin Dala Inland Dry Port. Yarjejeniyar ta tanadi cewa jihar za ta biya kuɗin hannun jarin ta ne ta hanyar gina ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, da samar da ruwa a wurin da ake ginawa a Zawachiki, Kano.
Sai dai, gwamnonin da suka gabace shi, Shekarau da Rabiu Kwankwaso, ba su yi wani aikin da yarjejeniyar ta tanada ba na gina waɗannan kayayyakin ba. Wannan rashin aiki ya kai ga cewa Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Nijeriya (Nigerian Shippers’ Council) ta yi barazanar soke yarjejeniyar da kamfanin a shekarar 2019 saboda rashin cimma yarjejeniyar mallakar.
Shigowar Ganduje Da Sauya Mallaka A Asirce
Sakamakon barazanar soke yarjejeniyar ya sa dole wanda ya kafa kamfanin, Ahmad Rabiu, ya nemi sabon abokin tarayya. A cikin wannan lokacin ne, a ranar 5 ga Maris, 2020, aka gudanar da wani taro na musamman na kamfanin Dala Inland Dry Port.
A cikin wannan taron, an cire duk tsoffin daraktocin kamfanin, an kuma naɗa ƴaƴan Ganduje uku da wani ɗan nasa na kut da kut mai suna Abubakar Bawuro, a matsayin sabbin daraktoci. An ba kowane ɗaya daga cikin ƴaƴan Ganduje hannun jari na kashi 20% kowanne, haka kuma aka ba Bawuro da Rabiu kashi 20% kowanne. Wannan shi ne lokacin da aka cire Jihar Kano gaba ɗaya daga cikin masu mallakar hannun jarin.
Kwangilar Biliyoyin Naira Da Kano Ta Biya Duk Da Ba Za Ta Amfana Ba
Bayan hannun jarin ya koma na ƴaƴansa, Ganduje, a matsayinsa na Gwamnan jihar, shi ya zartar da ƙwangilar gina wannan ababen more rayuwa da jihar Kano ya kamata ta gina tun 2006 a matsayin biyan hannun jarinta. A ranar 7 ga Yuli, 2020, an ba da kwangilar aikin gina waɗannan kayayyakin ga kamfanin FRI Construction Company Limited akan kuɗi kimanin Naira biliyan 2.3, wanda daga baya aka ƙara zuwa fiye da Naira biliyan 4.
Ma’ana, Ganduje ya ba da ƙwangilar aikin da jihar Kano ya kamata ta yi domin biyan hannun jarinta, amma a lokacin da aka ba da kwangilar, jihar ba ta da ko kashi 1% a cikin kamfanin, yayin da ƴaƴansa suka riƙe da kashi 60% tare da abokinsa Bawuro.
Yadda Aka Musanya Hannun Jarin Daga Ƴaƴansa Zuwa Abokinsa
Bayan shekaru biyu, a 2022, bayanan kamfanin a CAC sun nuna cewa an cire ƴaƴan Ganduje daga jerin masu hannun jari, an kuma miƙa hannun jarinsu ga Abubakar Bawuro. Wannan ya sa Bawuro ya zama mai kashi 80% na dukkan hannun jarin kamfanin, yayin da Ahmad Rabiu ya ke riƙe kashi 20%.
Jihar Kano Ta Nuna Rashin Jin Daɗi
Gwamnatin Jihar Kano ta yanzu, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ƙi amincewa da wannan canjin mallakar. Wani jami’i a ma’aikatar kasuwanci ta jihar, Bashir Uba, ya tabbatar da cewa a bayanansa, jihar har yanzu tana da hannun jarinta na kashi 20%. Ya bayyana cewa ba a taba fitar da tallace-tallace ko nuna aniyar sayar da hannun jarin ba, sannan cewa haƙiƙa jihar na neman ƙara hannun jarinta a kamfanin, ba ragewa ba.
Ya kuma ce ma’aikatun jihar na gudanar da bincike kan yadda Bawuro ya sami ikon mallakar kashi 80% na kamfanin.
Keta Dokoki
Masana a fannin shari’a sun bayyana cewa, duk wani yunƙuri na sayar da hannun jarin jihar dole ne ya bi tsarin doka wanda ya haɗa da amincewa da izinin majalisar jihar, da kuma fitar da tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai na ƙasa domin neman masu saye. Binciken ya nuna cewa ba a bi wannan tsari ba, wanda ke nuna cewa an yi wannan musayar mallaka ne a asirce kuma ba bisa ƙa’ida ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp